Da duminsa: Allah ya yiwa matar Sanata Kabir Gaya rasuwa

Da duminsa: Allah ya yiwa matar Sanata Kabir Gaya rasuwa

Shugaba Muhammadu Buhari ya jajantawa Sanata Kabiru Gaya mai wakiltan mazabar Kano ta kudu a majalisar dattawan tarayya bisa rasuwar uwargidarsa, Hajita Halima Gaya.

Shugaba Buhari, a jawabin da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya saki ya siffanta Hajiya Halima matsayin jajirtacciyar mace da ta sadaukar da rayuwarta wajen inganta ilimi.

Buhari ya yabawa irin hannun jarin da tasa wajen kafa makarantun kudi inda yace "Nazari ne mai kyau da ya kamata wasu su kwaikwaya."

"Ilimi kayan aikin cigaban zamani ne kuma babu kasar da ya kamata ta yi watsi da muhimmancin ilimi a rayuwarmu."

"Ina mai jajantawa Sanata Gaya da al'ummar jihar Kano. Allah ya kara musu hakuri."

Da duminsa: Allah ya yiwa matar Sanata Kabir Gaya rasuwa
Da duminsa: Allah ya yiwa matar Sanata Kabir Gaya rasuwa
Asali: Twitter

Hakazalika shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya aika sakon ta'aziyyarsa ga Sanata Kabiru Gaya.

Ya yi addu'a ya jikan mamaci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel