‘Yan Sandan Jihar Kaduna za su karo Jami’ai a lokacin bikin Sallah – CP Muri

‘Yan Sandan Jihar Kaduna za su karo Jami’ai a lokacin bikin Sallah – CP Muri

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Alhaji Umaru Muri ya yi kira ga mutane su bi dokokin da aka kafa domin kare kai daga cutar Coronavirus da ta zama annoba a fadin Duniya.

CP Umaru Muri ya bayyana cewa za su yi maganin duk wanda ya saba dokar zaman gida da shiga cinkoso a jihar Kaduna a yayin da musulman Duniya ke yin bikin karamar sallah.

Umaru Muri ya fitar da jawabi ta bakin jami’in da ke magana da yawun ‘yan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya na mai cewa za su ga bayan duk wani ko kungiyar da ta saba doka.

“Rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Kaduna su na sanar da mutane cewa ta tsara yadda za ta bi wajen ganin an bi dokar zaman-gidan da gwamnatin jiha ta sa domin yaki da annobar COVID-19 da kuma zuba dakaru domin maganin ta’adin migayu a lokacin bikin sallah a fadin jihar.”

KU KARANTA: Limami su takaita hudubar Idi a Jihar Kano - Gwamna Ganduje

‘Yan Sandan Jihar Kaduna za su karo Jami’ai a lokacin bikin Sallah – CP Muri
Gwamnan Jihar Kaduna Hoto: Twitter
Asali: Twitter

Jawabin Jalige ya kara da cewa: “A game da haka, rundunar ta baza jami’an ta-kife da masu fararen kaya su tsare ko ina, su kuma rika sa ido a wuraren da za a iya yin barna domin su tabbatar cewa an bi dokar zaman-gidan da aka kafa, sannan a samar da tsaro a cikin jihar”

A karshen kwamishinan ‘yan sandan ya ce: “Rundunar ta na kara tabbatarwa mutanen jihar Kaduna cewa a shirya ta ke ta saurari wani koke na ganin bayan duk wani mutumi ko kungiya da ke kokarin sabawa takunkumi da dokar hana shiga cinkoso a lokacin da ke wannan biki.”

Mohammed Jalige ya fitar da wannan jawabi ne a ranar Asabar, 23 ga watan Mayu, 2020, a madadin kwamishinan. Jami’in ya ce sun shirya yadda za su yi aiki a lokacin bikin sallah.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel