Gwamna Ayade ya zubar da hawaye yayinda ya dauke wa marasa karfi biyan haraji

Gwamna Ayade ya zubar da hawaye yayinda ya dauke wa marasa karfi biyan haraji

- Gwamna Ben Ayade ya tsame wasu mutane da kungiyoyi daga biyan haraji a jihar Cross Rivers

- Ayade ya bayyana hakan ne yayin rantsar da cibiyar sassautawa masu karamin karfi biyan haraji

- Gwamnan ya ce wannan na daga cikin kokarinsa na rage radadin COVID-19 a jihar

Gwamnan jihar Cross Rivers, Ben Ayade ya amince da a cire wasu mutane da kungiyoyi da suka fada cikin masu karamin karfi daga cikin masu biyan haraji.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Mayun 2020 yayin rantsar da kwamitin sassauci ga masu karamin karfi a jihar, Channels TV ta ruwaito.

Ayade yace duk wadanda ke kokarin samun na abinci basu cikin wadanda za su biya haraji a jiharsa.

Ayade ya fashe da kuka yayin da yake korafin yadda haraji ke takura wa masu karamin karfi a jihar.

Gwamnan ya ce bai taba sanin akwai jama'ar jihar da har yanzu suke rayuwa a gidan jinka ba.

Gwamna Ayade ya zubar da hawaye yayinda ya dauke wa marasa karfi biyan haraji
Gwamna Ayade ya zubar da hawaye yayinda ya dauke wa marasa karfi biyan haraji Hoto: The Sun
Asali: Twitter

"A shekaru biyar da nayi ina shugabanci, ban taba sanin cewa zan samu masu rayuwa a gidan jinka ba a jihata," yace.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Benue ta amince da sake bude wuraren bauta

Tsame masu karamin karfi daga biyan haraji tallafi ne. Ya shafi masu noma kadan, kasuwanci da masu ababen hawa na haya.

Ya ce masu siyar da abinci tare da duk wadanda ke gwagwarmayar samun na ci basu cikin wadanda za su biya haraji a jiharsa.

A wani labarin kuma, yayin da ma’aikatan kiwon lafiya ke shirin shiga yajin aiki a Kaduna, gwamnati ta bayyana cewa za ta cigaba da bude cibiyoyin kiwon lafiyar tare da kare ma’aikatan dake son zuwa aiki.

Gwamnatin ta bayyana haka ne a matsayin martani ga kokarin shiga yajin aiki da ma’aikatan ke yi, inda ta ce ba za ta lamunci duk wani bita da kulli daga wajen ma’aikatan ba.

Don haka tace bata amince da yajin aikin ba, kuma duk wanda bai je aiki ba ya yi asarar aikinsa kenan domin kuwa za’a dauki sunan kowanne ma’aikaci a ma’aikatar kiwon lafiya.

A dalilin haka gwamnati ta gargadi wadanda zasu shiga yajin aikin da kada su sake su tare kofofin asibitoci ko kuma kokarin hana mutane shiga asibitoci don a duba lafiyarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng