COVID-19: Muna kashe N40,000 zuwa N50,000 a kan kowanne gwaji - Farfesa Abayomi

COVID-19: Muna kashe N40,000 zuwa N50,000 a kan kowanne gwaji - Farfesa Abayomi

Kwamishinan lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi, ya ce gwamnatin jihar na kashe tsakanin N40,000 zuwa N50,000 a kan kowanne gwajin da ake wa mutum daya da ake zargin yana dauke da cutar coronavirus.

Ya ce a halin yanzu jihar ta kashe kusan naira miliyan 800 a gwajin samfur 16,000.

Ba a karbar ko sisin kwabo don yin gwajin cutar coronavirus a jihar Legas da sauran sassan kasar nan.

Abayomi, wanda ya sanar da hakan yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a kan halin da ake ciki dangane da annobar a jihar a ranar Alhamis, yace, "mun gwada samfur 16,000 a Legas, wanda shine mafi yawa a fadin Najeriya.

"Muna shirye-shiryen gwada mutum 1,000 a rana daya nan da wata daya zuwa biyu.

"A halin yanzu, gwamnati na yin gwaji kyauta kuma tana biyan daga N40,000 zuwa N50,000 na kowanne guda.

"Amma a yayin da muke son kara yawan gwajin, za mu roki rangwame ko ta hanyar inshora ko kuma gudumawa daga jama'a.

"A halin yanzu, gwamnatin jihar na samar gwaji kyauta ga kowanne mutum da ke bukatar gwajin a kowacce cibiyar gwaji."

COVID-19: Muna kashe N40,000 zuwa N50,000 a kan kowanne gwaji - Farfesa Abayomi
COVID-19: Muna kashe N40,000 zuwa N50,000 a kan kowanne gwaji - Farfesa Abayomi. Hoto daga SaharaReporters
Source: UGC

DUBA WANNAN: 'An sayar mana da 'yancinmu': Wasu sojoji sun yi Allah-wadai da Buratai

Ya ce Legas na samun hauhawar yawan masu cutar coronavirus saboda karuwar yawan cibiyoyin gwajin.

Ya ce Legas na da dakunan gwaji hudu wadanda suka fara aiki kusan watanni uku da suka gabata. Jihar na da wuraren karbar samfur har 20 a fadinta.

Jaridar Punch HealthWise ta ruwaito cewa, wuraren karbar samfur 20 din jihar duk sun daina aiki saboda rashin sinadarai.

A wani labari na daban, iyalan tsohon shugaban Najeriya, marigayi Umaru Musa Yar’adua sun bayar da gudunmawar kayan abinci da kayan kare kai daga kamuwa da kwayoyin cuta, PPE, ga hukumar kula da Abuja, FCTA.

Sun bayar da kayayyakin ne a matsayin gudunmawarsu wurin yaki da annobar coronavirus da ta adabi kasashen duniya ciki har da Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel