Abin kunya ne yadda ‘Yan Majalisa su ke sato dokokin Singafo – Sanata Sani

Abin kunya ne yadda ‘Yan Majalisa su ke sato dokokin Singafo – Sanata Sani

– Shehu Sani ya zargi ‘Yan Majalisa da sato dokoki daga wata kasar waje

– Tsohon Sanatan ya ce don lalaci wasu kan dauko dokokin kasar Singafo

– ‘Dan siyasar bai iya kama sunan wani wanda ya ke irin wannan aiki ba

Kwamred Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, ya nuna fushinsa game da wani hali na ‘yan majalisar kasar nan.

Shehu Sani ya fito shafinsa na Tuwita ne ya na yin tir da yadda ‘yan majalisa su ke sato dokokin kasar Singafo, su nemi su zuba a cikin dokokin Najeriya.

Ba yau Sani ya fara fitowa ya jefi ‘yan siyasar da zargi ko yin ba daidai ba. ‘Dan siyasar mai shekaru 52 ya saba jefa maganganu a shafukan sadarwa.

Sanata Shehu Sani ya zargi tsofaffin abokan aikinsa da lalaci, sai dai bai kama sunan wani ‘dan majalisa da ya ke yin irin wannan abin kunya da ya ce ba.

KU KARANTA: 'Dan Sanda ya ki karbar cin - hanci, ya gargadi maras gaskiya

Sani ya na cikin fitattun ‘yan majalisar tarayya a lokacin Bukola Saraki, ya kasance shugaban kwamitin da ke lura da bashi da aron kudi a gida da waje.

Legit.ng ta fahimci Kwamred Sani ya yi wannan magana ne yayin da jama’a su ka fara zargin wani sanatan APC da sato dokar waje a wani kudirinsa.

Ana zargin sanata Mohammed Musa da kinkimo kudirinsa na yi wa kafafofin sadarwan takunkumi daga kasar Kudu maso gabashin Nahiyar Asiyar.

Wasu sun yi wa ‘dan siyasar raddi, su ka zarge sa da cewa bai yi kokarin gyara hakan ba a lokacin da ya ke rike da kujerar sanata na tsawon shekaru hudu.

“Abin kunya ne yadda wasu ‘yan majalisarmu su ke dauko dokokin kasar Singafor sunkututum, su sa cikin kasarmu.” – Shehu Sani

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng