Babu batun taron sallar idi bana a birnin tarayya a Abuja – inji CFII

Babu batun taron sallar idi bana a birnin tarayya a Abuja – inji CFII

Yayin da bikin karamar sallah ya karaso, kungiyoyin addinai da su ka hada da kiristoci da musulmai sun yi zama da ministocin Abuja domin tsaida matsaya a kan yin taron sallar idi.

Sakataren kungiyar CFII ta limaman musulunci na reshen birnin tarayya Abuja, Is'haq Y. Zango, ya fitar da jawabi, ya bayyana sakamakon tattaunawar zaman da su ka yi da jami’an gwamnati.

“An samu wata muhimmiyar doguwar zama da ministan babban birnin tarayya Abuja Muhammadu Musa Bello da shugabannin kungiyoyin CAN na kirstoci da CFII na limaman Abuja da karamar minista, da wasu jami’an ma’aikatar lafiya, inda aka tattauna yiwuwar fita sallar idi.”

“Matsayar da aka cin ma a wajen taron shi ne a cigaba da yadda ake a yanzu saboda hujjojin da ma’aikatan kiwon lafiya su ka gabatar.” Inji Is'haq Y. Zango a madadin kungiyar ta CFII.

KU KARANTA: Masana sun ce rufe Mutane a gida zai iya kisa fiye da ta cutar COVID-19

“Kwamitin mutum bakwai zai zauna da wakilan CFII da CAN da za a kaddamar a karkashin babban hadimin minista, zai shawo kan hanyar da za a bi tukuna wajen bude dakunan ibada.”

“Wannan kwamiti da za a kafa zai yi maza ya kammala aikinsa ne a cikin ‘yan kwanaki kadan masu zuwa.” Sakataren limaman ya fitar da wannan jawabi ne a ranar 19 ga watan Mayu, 2020.

“Ana kira da cewa mu kara hakuri da bin dokokin hukuma, tare da kira ga mabiya su fahimci halin da ake ciki, su kuma dage da addu’o’i.” A karshe aka yi wa jama’a fatan shan ruwa lafiya.

A daidai wannan lokaci wasu gwamnonin Arewa sun bada damar mutane su fita su yi sallar idi. Sarkin Musulmi da wasu malamai da kungiyoyi irinsu MURIC ba su goyon bayan hakan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel