Bidiyon dan sanda na kin karbar cin hanci a wurin direba ya jawo cece-kuce

Bidiyon dan sanda na kin karbar cin hanci a wurin direba ya jawo cece-kuce

Wani bidiyon dan sandan kasar Ghana ya kawo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamani bayan yaduwarsa.

A bidiyon, an ga dan sandan na kin karbar cin hanci ko kuma kudin goro wanda direbobi suka saba bai wa 'yan sandan kan hanya. Ya ja kunnen direban tare da ce mishi kada ya kuskura ya kara mishi irin haka.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, har yanzu dai ba a gano sunan dan sandan ba amma an san ya fito ne daga yankin Volta kuma yana zama a garin 'Akan' saboda yaren 'Twi' da ya bayyana daga harshensa.

A bidiyon, dan sandan ya tsayar da abun hawa wanda ake kira da 'Mahama Camboo' don dubawa.

Ya bukaci lasisin tukin direban wanda direban ya gaggauta mikawa da wasu kudi a tare.

A take kuwa dan sandan ya fusata bayan ya ga kudin. A nan ya ce wa direban ya mayar da motarsa gefen titi kuma ya jirasa.

Bayan kankanin lokaci, dan sandan ya koma kan direban tare da tambayarsa dalilin da yasa ya bashi 'na goro'. A take kuwa direban ya fara bada hakuri tare da neman yafiya.

"Kudinka ba zai yi min komai ba saboda ina samun albashi fiye da kai. Ka san nawa ake biyana a wata?" Fusataccen dan sandan ya tambaya direban.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon wata ma'aikaciyar jinya da aka kama ta saci jinjiri

Kamar yadda bidiyon ya nuna, an nadesa ne a sirrance ba tare da direban ko dan sandan ya sani ba amma kuma sai aka ci karo da abun mamaki.

A wani labari na daban, mun ji cewa zafin kishi ya sa wata mata ta gutsure kunnen abokiyar zamanta da hakori yayin da suka ba wa hammata iska jihar a Jigawa da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Fada ya kaure a tsakanin kishiyoyin biyu saboda wata sa'insa da 'dan daya daga cikinsu ya haddasa kamar yadda jaridar Aminiya ta wallafa.

Wannan mummunan lamari ya auku ne a tsakanin matan wani mutum da a ke kira Dan Borno, masu suna Zubaida da Rabi, a cikin gidan mijin nasu da ke Unguwar Zai a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel