Tsaf APC za ta iya faduwa zaben gwamna a Edo da Ondo - Jigo a jam'iyyar ya bayyana dalili

Tsaf APC za ta iya faduwa zaben gwamna a Edo da Ondo - Jigo a jam'iyyar ya bayyana dalili

Har ila yau, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa (shiyyar arewa) da aka dakatar, Lawal Shuaibu, ya sake zargin shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, da take doka a harkokin gudanar da jam'iyyar APC.

Shuaibu ya ce irin karan tsaye da Oshiomhole ke yi wa doka zai iya jawowa jam'iyyar APC faduwa zaben gwamna a jihohin Edo da Ondo, kamar yadda ta faru a jihar Zamfara a zaben shekarar 2019.

"Tuntuni akwai kunbiya - kunbiya a yadda ake gudanar da harkoki a cikin jam'iyya," a cewar Shuaibu yayin da ya ke magana a kan zaben fidda 'yan takara a jihohin Edo da Ondo.

An kwace wa jam'iyyar APC dukkan kujerunta tare da mikasu ga jam'iyyar PDP a jihar Zamfara a wani hukunci da kotun koli ta yanke a 2019.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bisa dogaro da cewa jam'iyyar APC ta take doka yayin gudanar da zaben fidda 'yan takararta a jihar Zamfara.

A cikin wata wasika da Shuaibu ya wallafa ranar Laraba, ya yi gargadin cewa al'amura za su iya durkushewa a cikin jam'iyyar APC matukar Oshiomhole ya ci gaba da sabawa kundin mulkinta.

Shuaibu ya ce an sabawa doka wajen tabbatar da Waziri Bulama a matsayin mukaddashin sakataren jam'iyyar APC na kasa.

Kazalika ya yi zargin cewa ana kulla rashin gaskiya a zaben fidda dan takarar gwamna da jam'iyyar za ta yi a jihohin Edo da Ondo, lamarin da ya ce tsaf zai jawo jam'iyyar ta fadi zaben kujerar gwamna a jihohin.

Tsaf APC za ta iya faduwa zaben gwamna a Edo da Ondo - Jigo a jam'iyyar ya bayyana dalili
Oshimhole
Asali: Depositphotos

A ranar Laraba ne Legit.ng ta wallafa labarin cewa jam'iyyar APC mai mulki ta ce ma su son yin takarar gwamna a zaben da za a yi ranar 19 ga watan Satumba da 10 ga watan Oktoba a jihohin Edo da Ondo za su biya miliyan N22.5 a matsayin kudin fom din takara.

DUBA WANNAN: Buhari ya kori shugaban NECO da manyan jami'an hukumar 4

A cikin sanarwar da sakataren tsare - tsaren APC, Emma Ibediro, ya fitar a Abuja, jam'iyyar ta ce za ta fara sayar da fom ga ma su sha'awar takara gabanin gudanar da zaben cikin gida na fidda dan takara.

A cewar Ibediro, jam'iyyar APC za ta fara sayar da fom din takarar gwamna a jihar Edo daga ranar 20 ga watan Mayu zuwa ranar 2 ga watan Yuni, yayin da za ta fara sayar da na takarar gwamna a jihar Ondo daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa ranar 1 ga watan Yuli.

A cikin watan Fabrairu ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tsayar da ranar 19 ga watan Satumba da ranar 10 ga watan Oktoba a matsayin ranakun gudanar zabe a jihohin Edo da Ondo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel