Covid-19: Sarkin Musulmi ya yi umurnin kowa yayi Sallar Idi a gida

Covid-19: Sarkin Musulmi ya yi umurnin kowa yayi Sallar Idi a gida

- Sarkin Musulmi ya bayyana matsayarsa a kan yadda za a yi sallar Idin shekarar nan

- A yayin da sarkin Musulmin yace musulmai su yi sallarsu a gida don gujewa cunkoso, wasu gwamnonin arewa sun dage dokarsu don a yi sallar a jam'i

- Sarkin musulmin yace sallar idin ba farilla bace kuma idan har akwai kalubalen tsaro da ya hada da lafiya ana hakura ne kwata-kwata

Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa'ad ya bayyana matsayarsa a kan yadda za a yi sallar Idin shekarar nan

Alh Sa'ad Abubakar, wanda shine shugaban majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci na kasa, ya bada umarnin cewa Musulmi su yi sallarsu a gida don dakile yaduwar cutar coronavirus.

Amma kuma, wasu gwamnonin arewa sun sassauta doka a jihohinsu don bai wa Musulmi damar yin sallar Idin a jam'i.

Sallar idi: An samu sabani tsakanin sarkin Musulmi da wasu gwamnonin arewa
Sallar idi: An samu sabani tsakanin sarkin Musulmi da wasu gwamnonin arewa Hoto: Vanguard
Source: UGC

A farkon makon nan na gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da a yi sallar Juma'a ta ranar 22 ga watan Mayu da kuma sallar Idi.

A ranar Laraba, gwamnan jihar Bauchi, Gwamna Bala Mohammed ya amince da yin sallar idi a jihar yayin da ya bukaci a kiyaye dokar nesa-nesa da juna tare da saka takunkumin fuska.

Sauran jihohin da suka bi ayari sun hada da Yobe, Jigawa, Gombe, Borno da Zamfara.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Sai mun kawo karshen dukkan damuwar Kanawa - Ganduje

A wata takarda da mataimakin sakataren majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci, Farfesa Salisu Shehu, ya fitar a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, ya ce "sallar Idi ba wajibi bace kuma ba a son yin ta matukar akwai wata barazana ta tsaro ko annoba."

"Musulmai su yi sallar idi amma yayin da suke kiyaye dokokin tsafta, saka takunkumin fuska da kuma nesa-nesa da juna."

"A wannan halin, ana bukatar a kiyaye taron jama'a ballantana irin na idi."

"Amma kuma a jihohi da ba a amince da yin sallar ba, ana kira ga Musulmi da su bi doka yayin da suka saka wa a ransu cewa niyyarsu za ta samar musu da lada."

*Mun sauya wasu abubuwa cikin labarin nan musamman bangarorin cewa gwamnoni sun samu sabani da Sarkin Musulmi. Ayi mana afuwa maganar ba haka take ba

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel