Zamfara: Matawalle ya bayyana yadda zai 'yi maganin' 'yan bindiga

Zamfara: Matawalle ya bayyana yadda zai 'yi maganin' 'yan bindiga

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya bai wa jama'ar jiharsa tabbacin cewa manoman jihar sai sun koma gonakinsu a bana.

Kamar yadda yace suna nan suna tsara yadda za a yi, "Da yardar Allah ina tabbatar wa Zamfarawa cewa wannan damunar kowa zai yi noma."

A yayin tattaunawa da BBC a shafukan sada zumunta, gwamna Matawalle ya ce yana ci gaba da tattaunawa da jami'an tsaro har da kwamishinan 'yan sanda.

Ya ce wasu tubabbun 'yan ta'adda sun same shi tare da nuna matukar alhininsu a kan yadda hare-haren nan ke ci gaba.

Sanannen abu ne cewa, mutanen karkara ne kadai ke iya noma a jihar Zamfara da wasu jihohin masu makwabtaka da ita sakamakon takura su da 'yan bindiga suka yi.

Matawalle ya ce: "Tubabbun 'yan bindigar da muka yi sulhu dasu sun tabbatar da cewa da kansu za su bi sauran takwarorinsu wadanda ake zargi da kai harin don su tsawatar musu a karon karshe."

A cewarsa, "Na bada damar a ba da eka 100,000 wacce kungiyar manoman auduga ta bukata don bunkasa noman auduga da rage yawan marasa aikin yi wanda babban bankin Najeriya zai tallafa wa."

Zamfara: Matawalle ya bayyana yadda zai 'yi maganin' 'yan bindiga
Zamfara: Matawalle ya bayyana yadda zai 'yi maganin' 'yan bindiga. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Covid-19: Sabbin mutum 226 sun kamu a Najeriya, jimilla 6401

Ya tabbatar da cewa Ubangiji ne ya hore wa jihar Zamfara fadin kasa da albarkar kasar noma.

Amma Bello Matawalle ya ce, matukar gwamnonin yankin basu daura damarar magance rikice-rikicen da kansu ba, za ta yiwu a ci gaba da samun wannan matsalar ta tabarbarewar tsaro a yankin.

"Idan taro za a yi da irin wadannan mutane da suka ce sun yarda da sulhu, to mu gwamnonin sai mun taru gaba daya. Kuma mu tabbatar da mun aiwatar da duk matsayar da muka cimma," Gwamna Matawalle yace.

Ya kara da cewa, babu wanda zai zo har gida ya magance wa al'ummarsu matsala face su gwamnonin da kansu.

"Duk yadda muke tunanin za mu sa wani ya dauka mataki, wallahi ba za su yi kamar yadda muke so ba. Wannan ce gaskiyar lamarin," Gwamnan yace.

Bello yace, masu kai hare-haren kullum kukansu shine an mayar da su koma baya, kamar babu su gaba daya. Ba a sanya su cikin shirye-shirye da romon damokaradiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel