Yaki da yan bindiga: Dakarun hadaka sun isa jahar Katsina don gudanar da aiki na musamman

Yaki da yan bindiga: Dakarun hadaka sun isa jahar Katsina don gudanar da aiki na musamman

An tsaurara matakan tsaro a jahar Katsina biyo bayan wasu manyan motocin yaki kirar Armoured Personnel Carrier da suka shirya tsaf don kaddamar da hari a kan yan bindiga.

Punch ta ruwaito wasu jami’an tsaro na hadaka ne za su yi amfani da wadannan motoci domin gudanar da aiki na musamman daya danganci yaki da miyagun yan bindiga a jahar Katsina.

KU KARANTA: Duk da matsalar Corona, likitoci sun shiga yajin aikin dindindin a Najeriya

A jibge motocin ne a sansanin horas da yan bautan kasa dake titin Mani, kuma a sansanin ne aka sauke kwararrun jami’an tsaron na musamman da za su jagoranci hari a kan yan bindigan.

Babban jami’in Yansanda, DIG Abdul Majeed Alli ya ce rundunar ta kunshi Yansanda, Sojoji, jami’an hukumar DSS da kuma jami’an hukumar tsaro ta farin kaya NSCDC.

Yaki da yan bindiga: Dakarun hadaka sun isa jahar Katsina don gudanar da aiki na musamman
Sojoji Hoto: Punch
Source: UGC

Isar sa jahar Katsina ke da wuya, kai tsaye DIG Alli ya zarce shelkwatar Birget din Sojan kasa inda ya tattauna da manyan hafsoshin Sojan na tsawon sa’a 1, haka yayi da DSS da NSCDC ma.

Kazalika kwamandan aiki na musamman na rundunar Sojan sama, AVM C.A Ohio ya isa jahar Katsina a ranar Talata don ganin yadda za su tsara harin da za su kaddamar ma yan bindigan.

Ohio yace ya kai ziyarar ne don tabbatar da Sojojin sama sun taka muhimmin rawa a wannan hari da za’a kaddamar, inda yace sun tanadi jiragen yaki guda uku saboda wannan aiki.

Bayan zagayensa, DIG Alli ya tsaya a sansanin da aka sauke dakarun na musamman, inda ya nemi su gudanar da aikinsu cikin nuna kwarewa tare da yin abin da ya kai su.

“Na zo nan ne domin na basu kwarin gwiwa, an basu horaswa na musamman saboda wannan aiki, kuma zasu gudanar da aikin tare da hadin gwiwar Sojojin kasa, DSS da jami’an NSCDC. Mai yiwuwa su dauki tsawon lokaci, ko gajeren lokaci, amma zan so su gama cikin lokaci.” Inji shi.

Daga karshe Alli ya nemi hadin kan jama’a wajen basu bayanan sirri game da ayyukan yan bindigan, kuma ya ce sun dauki matakan hana yan bindigan tserewa ta iyakokin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel