COVID-19: Sarkin Bauchi ya soke hawan sallah

COVID-19: Sarkin Bauchi ya soke hawan sallah

- Sarkin Bauchi, mai martaba Rilwanu Sulaiman Adamu, ya soke hawan sallah a jihar

- Wannan ya zo ne bayan gwamna Bala Mohammed ya dage dokar hana zuwa wuraren bauta

- Sarki Rilwanu, ya ce za a koyar da limaman jihar Bauchi yadda za su tabbatar da an bi dokar nesa-nesa da juna a yayin sallar Idi

Mai martaba sarkin Bauchi, wanda shine shugaban masu sarautar gargajiya na jihar ya soke hawan daba a yayin sallar Idi mai zuwa.

Basaraken ya bada wannan umarnin ne yayin taron da yayi da masu ruwa da tsaki a kan annobar COVID-19 wanda aka yi a masaukin bakin gwamnatin jihar, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Ya ce akwai babbar bukatar hana taro mai yawa don kowa abun zargi ne a kan cutar coronavirus.

Rilwanu ya kara da cewa, za a wayar da kan dukkan limaman jihar a kan yadda za su tabbatar da dokar nesa-nesa da juna yayin sallar Idi a fadin jihar.

COVID-19: Sarkin Bauchi ya soke hawan sallah
COVID-19: Sarkin Bauchi ya soke hawan sallah Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Bauchi ta hana fita wuraren bauta a jihar tun cikin watan Afirilu don dakile yaduwar annobar coronavirus.

A yau dai Gwamna Bala Mohammed ya sanar da dage dokar a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, 20 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya bayyana ma Buhari muhimman hanyoyi 2 da zai bi don inganta rayuwar yan Najeriya

Amma kuma yace an dage dokar ne na makonni biyu kacal. Gwamnan ya ce dage dokar ya biyo bayan bayyana wa da hukumar kiwon lafiya ta duniya tayi na cewa akwai yuwuwar annobar ta dade.

Ya kara da cewa wasu jihohin yankin arewa maso gabas din sun dage dokar.

Mohammed ya kara da cewa dage dokar na makonni biyu na dauke da sharuddan da suka hada da saka takunkumin fuska, samar da sinadarin tsaftace hannu da kuma ruwa mai tsafta a wuraren bauta.

Wannan mataki na gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin takwarorinsa suka janye dokar kulle a jihohinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel