'Yan ta'adda sun halaka masu buda baki 8 a wani harin da suka kai Masallaci

'Yan ta'adda sun halaka masu buda baki 8 a wani harin da suka kai Masallaci

Wasu 'yan bindiga sun budewa masu bauta wuta a yammacin Talata a wani masallaci da ke tsakiyar Afghanistan.

A take suka halaka mutum takwas da ke buda baki inda suka raunata mutum biyar, jami'ai suka tabbatar.

"Wasu 'yan bindiga sun budewa masu bauta wuta a yayin da suke buda baki," Wahida Shahkar, mai magana da yawun gwamnan yankin Parwan ta sanar a wannan watan mai alfarma.

Ma'aikatar al'amuran cikin gida ta tabbatar da barin da aka kai yankin Parwan. An dora laifin da 'yan ta'addan Taliban. Amma kuma 'yan ta'addan sun musanta hannunsu a cikin harin tare da dora laifin a kan jami'an tsaron Afghan.

Tuni majalisar dinkin duniya ta ja kunne a kan yuwuwar karuwar tashin hankula a yankin Afghanistan.

'Yan ta'adda sun halaka masu buda baki 8 a wani harin da suka kai Masallaci
'Yan ta'adda sun halaka masu buda baki 8 a wani harin da suka kai Masallaci Hoto: Bioreports
Asali: UGC

Wani hari mai matukar bada mamaki ya auku a makon da ya gabata a wani asibitin haihuwa da ke Kabul. An rasa rayukan mutum 24 wadanda suka hada da jarirai.

An samu ci gaban tashin hankali a kasar tun bayan ranar 29 ga watan Fabrairu.

A ranar Talata da ta gabata, jami'an tsaro sun yi artabu da mayakan Taliban a wurin birnin Kunduz, daya daga cikin biranen da mayakan Taliban din suka dinga kallo don hara kuma sun taba kama garin har sau biyu.

Da kokarin dakarun sojin sama ne jami'an tsaro suka fatattaki mayakan ta'addancin.

Assadullah Khalid, mukaddashin ministan tsaro, ya ce yayin da ya kai ziyara, ya samu gawawwakin yan ta'adda 50 da na jami'an tsaro takwas da suka rasu.

Mayakan Taliban sun yi watsi da kiran da ake ta musu don yada makamai da gwamnatin Afghan. Sun musanta hannunsu a harin gidan haihuwan kuma gwamnatin Amurka ta zargi ISIS da kai harin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Bauchi ya bude wuraren bauta, za a yi sallar Idi

Gwamnatin Amurka ta tura tawaga ta musamman ga Khalilzad, Doha da Kabul don assasa tattaunawa tsakanin mayakan Taliban da gwamnatin Afghan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel