Nahiyar Afrika: WHO ta jero kasashen da ake da karancin masu COVID-19
- Mutum sama da 90, 000 COVID-19 ta kwantar a fadin kasashen Afrika
- Najeriya, Kamaru da Ghana su na cikin kasashen annobar ta yi kamari
- Coronavirus ta hallaka mutane fiye da 1, 000 a wasu manyan kasashe 5
A yau ranar Laraba, 20 ga watan Mayu, 2020, hukumar lafiya ta Duniya watau WHO ta fitar da rahoto cewa masu dauke da kwayar cutar COVID-19 a nahiyar Afrika sun haura 90000.
WHO ta fitar da wannan rahoto ne daga babban ofishin ta na nahiyar Afrika da ke birnin Brazzaville a kasar Congo. Rahoton ya fito ta shafin ofishin na tuwita a @WHOAFRO.
A cewar hukumar kasashen Lesotho, Comoros, da Seychelles ne su ke da karancin masu dauke da cutar. Har yanzu a Lesotho mutum guda rak aka samu labarin ya kamu da Coronavirus.
A kasar Comoros, akwai mutane 11 da aka tabbatar cutar ta harbe su. A Seychelles ma ana da mutane 11 da ke dauke da COVID-19, sai dai babu wanda annobar ta ga bayansa a kasar.
KU KARANTA: Bincike ya nuna abin da ke kashe mutane a Jihar Kano
Coronavirus ta kashe mutum guda a Comoros, a kasar Lesotho kuwa har yanzu alkaluma sun nuna babu wanda ya mutu sanadiyyar cutar. Maras lafiyan 33, 000 su ka warke a Afrika.
Alkaluman na WHO sun kuma bayyana cewa kasar Afrika ta kudu, Aljeriya, da Najeriya ne kam gaba wajen masu dauke da Coronavirus. Kasashen su na da masu jinya har kusan 30, 000.
A ranar Talata, akwai mutane 16433 da ke jinyar cutar a Afrika ta kudu. Mutane 7201 ake da labarin sun kamu da COVID-19 a Aljeriya. A Najeriya kuma akwai 6175 da cutar ta harba.
Mutane 286, 555, 191 ake da labarin sun mutu a wadannan kasashe uku. A kasar Ghana kuwa ana da labarin mutane 5, 735 da su ke dauke da cutar, a Kamaru ana da mutane kusan 3, 600.
Abin da hakan ya ke nufi shi ne mutane 1101 wannan cutar ta kashe a kasashen Afrika ta kudu, Aljeriya, da Najeriya, Kamaru da Ghana. A Duniya sama da mutum 300, 000 cutar ta kashe.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng