‘Yan Sanda sun tsare, wanda ya zagi Lai Mohammed a gidan rediyo

‘Yan Sanda sun tsare, wanda ya zagi Lai Mohammed a gidan rediyo

Wata kungiyar tsaro da kare hakkin Bil Adama ta CDHR ta na zargin cewa jami’an ‘yan sanda sun tsare wani ‘dan jarida a kasar mai suna Rotimi Jolayemi, ba tare da hakkinsa ba.

CDHR ta jefi sashen bincike na rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke babban birnin tarayya na Abuja da tsare Rotimi Jolayemi na tsawon kwanaki 12 saboda ya zagi Lai Mohammed.

A cewar CDHR, wannan bawan Allah wanda aka fi sani da Oba Akewi ya fada hannun jami’an tsaro ne bayan ya rera wani wake a gidan rediyo wanda ya soki babban ministan kasar.

Shugaban wannan kungiya na kasa, Osagie Obayuwana ne ya yi wannan ikirari a wani jawabi da ya fitar a ranar Litinin din makon nan kamar yadda mu ka samu labari a jaridar Punch.

Dr. Osagie Obayuwana ya ce: “Ana cewa ‘yan sanda sun kama Jolayemi ne da umarnin ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, saboda wata waka da ya yi da ta soke sa.”

“Akwai damuwa ace Alhaji Lai Mohammed ya na da hannu wajen tsare mista Jolayemi da mai dakinsa Dorcas Jolayemi, da ‘ma yanuwansa biyu da aka garkame na tsawon kwanaki.”

KU KARANTA: Yadda jama'a su ke juya abin da na fada, su na yi mani karya - Lai

‘Yan Sanda sun cafke, tsare, wanda ya zagi Lai Mohammed a gidan rediyo
Alhaji Lai Mohammed. Hoto: Pulse
Asali: Facebook

Osagie Obayuwana ya ce an tsare wadannan mutane na kwanaki biyu zuwa tara a hannun ‘yan sanda. Shi kuwa ‘dan jaridar ya shafe kwanaki goma sha biyu ya na garkame har yanzu.

“Tun da Jolayemi ya mika kansa gaban babban ofishin ‘yan sanda da ke Ilorin, a jihar Kwara a ranar 6 ga watan Mayu, 2020, har yanzu ana cigaba da rike shi, bayan kwanaki 12.”

Yau mako biyu kenan da aka kama matashin. Shugaban kungiyar ta CDHR mai zaman kanta, ya bayyana cewa ba a gurfanar da ‘dan jaridar a kotu ba, kuma ba a bada belinsa ba.

A Najeriya, daure ‘yanuwan ‘dan jarida domin ya fito, ya sabawa dokar kasa inji kungiyar. A bangarensa, mai magana da yawun ministan labaran, Segun Adeyemi ya karyata zargin.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kwara, Okasanmi Ajayi ya shaidawa Punch cewa bai da labarin an kama ‘dan jaridar. Hukumomi sun nuna cewa ba su da labarin tsare wannan mutumi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel