Frankline Ndifor: COVID-19 ta ga bayan wanda ya ke warkar da 'Yan Kamaru

Frankline Ndifor: COVID-19 ta ga bayan wanda ya ke warkar da 'Yan Kamaru

- Frankline Ndifor mai shekaru 39 ya mutu bayan kamuwa da Coronavirus

- Ndifor wanda Fasto ne ya taba tsayawa takarar Shugaban kasan Kamaru

- Faston ya na ikirarin ya kan yi wadanda su ka harbu maganin COVID-19

Wani limamin kirista mai suna Frankline Ndifor wanda ya ke da’awar warkar da masu dauke da Coronavirus, ya mutu a sakamakon harbuwa da wannan mummunar cuta a Kamaru.

Frankline Ndifor mai shekara 39 da haihuwa ya cika ne a ranar Asabar, 16 ga watan Mayu, 2020. Mabiya sun toshe hanyar shiga gidan faston da ke cikin garin Douala bayan ya mutu.

Gwamnan Douala ya bayyana cewa sai da ya baza jami’an tsaro sannan aka iya daukar gawar limamin. Mabiya sun yi ta addu’o’i da nufin ganin ya farfado daga mutuwar da ya yi.

VOA ta rahoto cewa mabiya su kan cika cocin marigayin na Kingship International Ministries domin ya ba su maganin cutar COVID-19. A karshe wannan cutar ce ta zama ajalinsa.

KU KARANTA: COVID-19 ta harbi wani Fasto mai kokarin ba mutane magani

Rahoton ya bayyana cewa an bizne Frankline Ndifor ne a gaban gidansa bayan ta tabbata cewa ya cika. An rufe malamin ne a ranar Asabar din da ya mutu, ba tare da an ajiye gawarsa ba.

Dr. Gaelle Nnanga, shi ne likitan da aka kira ya duba fasto Ndifor bayan da ya fara fama da matsalar numfashi. Wannan likita ya ce maras lafiyan ya rasu mintuna da fara dubasa.

Wani daga cikin mabiyan marigayin mai suna Rigobert Che ya shaidawa ‘yan jarida cewa faston ya yi masa addu’a tare da wasu dinbin mutane da ake zargin sun kamu da Coronavirus.

“Yanzu da ya mutu, ban san yadda mutanen da ya ke yi wa magani za su warke ba.” Inji wani daga cikin mabiyan mamacin. Yau kwana uku kenan da rasuwar wannan bajimin shehi.

Daily Mail ta rahoto wani mabiyi na marigayin mai suna Akere Muna ya na kokawa da rashin Ndifor. Ya hau shafin tuwita ya na cewa: “Fasto Franklin Ndifor Afanwi, har an tafi.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel