Kar ka bari a yi Sallar Idi a Kaduna - Sheikh Gumi ya aikawa El-Rufa'i sako

Kar ka bari a yi Sallar Idi a Kaduna - Sheikh Gumi ya aikawa El-Rufa'i sako

Sheikh Ahmad Gumi, fitaccen malamin addini, ya ce bai kamata a bar jama'a su halarci Sallar Eidi a jam'i ba a yayin da ake kokarin dakile yaduwar cutar korona.

Malamin addinin ya bayyana hakan ne yayin da ya ke ganawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Kaduna bayan kammala taro da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

A cewarsa, Sallar Eidi, wacce ake yi bayan kammala azumin Ramadana, za ta iya bata kokarin gwamnati na shawo kan cutar korona.

Gumi ya ce kokarin gwamnati ne ya sa ba a samu yawaitar mace - mace a Kaduna ba bayan bullar annobar korona a jihar.

Ya ce Najeriya ba kamar kasar Saudiyya ba ce da za a iya sarrafa taron jama'a a wurin ibada ba tare da bayyana cewa cutar za ta yadu cikin sauri ta hanyar sallah a jam'i.

"Da zarar an bar jama'a su fito domin yin Sallah, dubban jama'a za su fito ta yadda ba zai yiwu a sarrafasu ba. Mun shafe kusan wata biyu a karkashin dokar kulle, bai kamata rana daya ta zama silar lalacewar duk nasarorin da aka samu a baya ba," a cewarsa.

"Kaduna na daga cikin jihohin arewa da ake da karancin ma su cutar korona. Mu na ganin yadda daruruwan jama'a ke mutuwa a jihohi kamar Sokoto, Katsina, Kano, Yobe, Borno.

"Amma Alhamdulillah, saboda dokar kulle da aka saka da wuri a jihar Kaduna, mu na da karancin ma su dauke da kwayar cutar idan aka kwatanta da sauran jihohi. Babu wanda zai musanta hakan," kamar Sheikh Gumi ya fada.

Kar ka bari a yi Sallar Idi a Kaduna - Sheikh Gumi ya aikawa El-Rufa'i sako
Sheikh Gumi
Asali: Depositphotos

Gumi ya ce shi da sauran Malaman addini a jihar Kaduna sun bawa gwamnati shawara a kan matakin da ya kamata ta dauka.

DUBA WANNAN: 'Da amincewar ministan noma' - Mohammed Bello ya magantu a kan zargin sayen kango a N7bn

Kazalika, ya kara da cewa ruwan gwamnati ne ta yi aiki da shawararsu ko kuma ta dauki matakin da ya dace.

A cewarsa, "ya na da muhimmanci a wurin gwamnati ta tuntubi sauran ma su ruwa da tsaki da suka hada da sarakunan gargajiya da sauran kwararru da ke jihar Kaduna domin jin ra'ayinsu."

Ya zuwa yammacin ranar Litinin, akwai jimillar mutane 145 da ke dauke da kwayar cutar korona a jihar Kaduna.

A ranar Litinin ne gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya amince a gudanar da Sallar Eidi a Masallatai duk da tsawaita dokar kulle da sati biyu da shugaban kasa ya yi a jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel