'Da amincewar ministan noma' - Mohammed Bello ya magantu a kan sayen kango a N7bn

'Da amincewar ministan noma' - Mohammed Bello ya magantu a kan sayen kango a N7bn

Mohammed Bello, babban sakatare a ma'aikatar kimiyya da fasaha, ya musanta zargin badakalar kudin da ya ce ana kokarin rataya ma sa.

A makon jiya ne gwamnatin tarayya ta fara tuhumar Bello bisa zarginsa da tafka badakala lokacin da ya ke zaman babban sakatare a ma'aikatar noma da raya karkara.

Ana zarginsa da sayen wani kango domin amfanin ma'aikatar noma a kan zunzurutun kudi da yawansu ya kai biliyan N7 ba tare da bin ka'ida ba.

Da ya ke amsa tuhumar da ake yi ma sa, Bello, ya bayyana cewa da amincewar ministan harkokin noma, Sabo Nanono, da majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) aka sayi kangon.

A cikin wata wasika da ya rubuta a ranar 14 ga watan Mayu, Bello ya ce an bi dukkan ka'idojin da su ka dace kafin kashe duk wani kudi a lokacin da ya ke sakatare a ma'aikatar noma.

"Babu gaskiya ko kadan a cikin zargin da ake yi min, na mika dukkan hujjojin kare kaina daga zargin.

"Duk da doka ba ta bani damar fitar da dukkan bayanan kudi na ma'aikatar noma ba, ina son sanar da cewa babu wani kudi da ya fita daga ma'aikatar ba tare da bin ka'idoji da dokokin gwamnati ba.

'Da amincewar ministan noma' - Mohammed Bello ya magantu a kan sayen kango a N7bn

Mohammed Bello
Source: UGC

"Na kasance babban sakatare a ma'aikatar noma daga ranar 10 ga watan Janairu, 2019, zuwa ranar 18 ga watan Disamba, 2019 a saboda haka ba ni da alhakin duk wani abu da ya faru a ma'aikatar kafin ranar 10 ga watan Janairu, 2019."

DUBA WANNAN: Korona a Najeriya damfara ce kawai - Ma su jinyar da aka sallama

"An bi ka'ida wajen sayen ginin. Mun aika takardar neman izini zuwa ofishin sakataren gwamnatin tarayya bayan amincewar ministan ma'aikatar noma da raya karkara."

"Sakataren gwamnati ya gabatar da takardar a gaban majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) kuma ta amince da sayen wurin," a cewar Bello.

Bello ya zargi ministan noma da Mu'azu Abdulkadir, babban sakataren ma'aikatar na yanzu, da kitsa zargin da ake yi ma sa.

"Wadannan mutane ne ke zargin cewa kangon da aka saya bai dace ya zama ofis ba," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel