Operation Lafiya Dole sun ga bayan Boko Haram a wani Kauyen Nganzai

Operation Lafiya Dole sun ga bayan Boko Haram a wani Kauyen Nganzai

- Rundunar Operation Lafiya Dole ta hallaka wasu ‘Yan Boko Haram

- Sojojin kasa sun ce sun kashe ‘Yan ta’adda rututu a yankin Nganzai

Wasu dakaru na Operation Lafiya Dole sun ga bayan wasu ‘yan ta’addan ISWAP watau Boko Haram rututu, sun kuma yi nasarar ruguza makamansu a yankin Nganzai a Borno.

Sojojin Najeriya sun fitar da jawabi a ranar Talatar nan cewa sun hallaka sojojin ta’addan ne a wani kauye da ake kira Gajigana cikin karamar hukumar Nganzai da ke jihar Borno.

Rundunar sojin kasar na OPERATION Operation Lafiya Dole sun ce sun samu labarin mayakan Boko Haram ne daga wani kauye, daga nan su ka yi maza su ka far ma ‘yan ta’addan.

A wannan hari da sojin su ka kai ta sama da kasa a ranar 17 ga watan Mayu, sun budawa Boko Haram wuta, su ka kashe da-dama daga cikinsu, sannan su ka ruguza kayan aikinsu.

KU KARANTA: An kashe 'Yan ta'adda a wani gumurzu da aka yi da Sojoji a Baga

Daga baya wasu dakarun sun kutsa inda ‘yan ta’adda su ke, inda su ka yi nasarar ruguza wasu manyan bindigogi da ‘yan ta’addan su ke ji da su a wani kauye da ake kira Mitturu.

Makaman da aka samu a wannan kauye sun kunshi bindigogin AK-47 biyu, casbi da-dama na harsashi, da wasu kananan bindigogin hannu, sai kuma wani bam na LG3 guda daya.

Shugabannin sojojin kasar sun taya dakarun Operation Lafiya Dole murnar wannan gagarumar nasara da su ka samu a gwabzawar da su ka yi da ‘yan ta’addan ISWAP/Boko Haram.

Kamar dai yadda aka saba, an yi kira ga sojojin kasan su dage wajen kakkabe ragowar ‘yan ta’addan da su ka yi saura, su ke addabar yankin na arewa maso gabashin Najeriya.

A cikin ‘yan kwanakin nan, sojojin Najeriya sun yi nasara a kan miyagu da ‘yan ta’addan a jihohin Borno, Ribas, Delta, Nasarawa, Zamfara kamar yadda rahotanni su ka bayyana mana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel