Shugaba Buhari ya nada Kashim Ibrahim-Imam shugaban TETFUND

Shugaba Buhari ya nada Kashim Ibrahim-Imam shugaban TETFUND

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Kashim Ibrahim-Imam a matsayin shugaban hukumar TETFUND.

Adamu Adamu, ministan ilimi, ya sanar da wannan nadin a wata wasika da jaridar The Cable ta samu a ranar Litinin.

Kamar yadda wasikar ta bayyana, nadin Ibrahim-Imam ya fara aiki ne daga ranar 14 ga watan Mayun 2020.

Adamu ya bayyana cewa, shugaban zai kwashe shekaru hudu a wannan mukamin wanda za a iya sabunta masa idan wa'adinsa ya cika, amma bayan an gamsu da aikinsa na karon farko.

Shugaba Buhari ya nada Kashim Ibrahim-Imam shugaban TETFUND

Shugaba Buhari ya nada Kashim Ibrahim-Imam shugaban TETFUND Hoto: The Cable
Source: UGC

"Na rubuto wannan wasikar ne don in sanar da kai cewa shugaban kasa Muhammadu ya amince da nada ka a matsayin shugaban hukumar TETFUND daga ranar 14 ga watan Mayun 2020," wasikar ta bayyana.

"Nadin na shekaru hudu ne a karon farko kuma ana iya sabunta shi bayan an gamsu da aikinka a wa'adin farko.

"Dokokin aikin da albashin duk daya ne da na ayyukan gwamnatin Najeriya. Ina tayaka murna tare da maka fatan nasara."

Ibrahim-Imam ne dan takarar kujerar gwamnan jihar PDP a jihar Borno a shekarar 2003 da 2007.

Amma kuma a dukkan takarar ya sha kaye a hannun Ali Modu Sheriff na jam'iyyar ANPP.

KU KARANTA KUMA: Take doka: Jami'an tsaro sun damke Yusuf Sambo Rigachukun da dansa

A wani labari na daban, ministan sufurin Najeriya, Rt. Hon. Rotimi Amaechi ya bayyanawa ‘yan jarida yadda rashin aiki da zaman kashe wando ya yi sanadiyyar jefa sa cikin harkar siyasa ba don ya yi niyya ba.

Rotimi Amaechi ya yi hira da jaridar The Punch inda ya shaida cewa burinsa da farko a rayuwa shi ne ya zama ‘dan jarida ko kuma lauya, amma a karshe sai ya kare da zama ‘dan siyasa.

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya ke cewa bai shiga siyasa domin ya kawo karshen matsalolin kasar nan ba. Ministan ya bayyana cewa a gaskiya zaman kashe wando ne kawai ya matsa masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel