Korona: Sabbin mutane 216 sun karu, 33 a Katsina, Jimilla ta haura 6,000

Korona: Sabbin mutane 216 sun karu, 33 a Katsina, Jimilla ta haura 6,000

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar da cewa karin sabbin mutane 216 ne aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

A cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin 11:53 na daren ranar Litinin a shafinta na tuwita, ta fitar da jerin jihohi da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a kowacce jiha kamar haka;

74-Lagos

33-Katsina

19-Oyo

17-Kano

13-Edo

10-Zamfara

8-Ogun

8-Gombe

8-Borno

7-Bauchi

7-Kwara

4-FCT

3-Kaduna

3-Enugu

2-Rivers

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:53 na daren ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 6175 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

An sallami mutane 1644 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 191.

DUBA WANNAN: Korona a Najeriya damfara ce kawai, wasan kwaikwayon da ba a tsara shi da kyau ba - Mai jinyar da aka sallama

A ranar Litinin ne gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da bawa al’ummar jahar Kano daman gudanar da sallolin Juma’a tare da sallar Idi, duk da dokar zaman gida da gwamnatin tarayya ta tsawaita a Kano.

Babban mashawarcin gwamnan a kan harkar watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a shafinsa na tuwita.

Yakasai yace gwamnatin ta yanke wannan shawara ne bayan wata doguwar tattaunawa da ta yi da manyan Malamai guda 30 daga bangarorin Musulunci daban daban a fadar gwamnatin.

Daga karshe gwamnan ya amince da shawarwarin da aka yanke wurin, don haka ya amince za’a cigaba da dokar zaman gida, kuma za’a cigaba da dage dokar a ranakun Litinin da Alhamis.

Haka zalika gwamnatin ta bada izinin a bude Masallatan Juma’a a duk mako, kuma a gudanar sallar Idi a karamar sallar bana, amma da sharudda kamar haka;

i- Duk wanda zai shiga Masallacin Juma’a sai ya sanya takunkumin fuska

ii- Duk wanda zai shiga sai ya wanke hannuwansa da sanitizer

iii- Dole sai an raba sahu a cikin Masallatan

iv – Dole ne a rage tsawon huduba don rage taron jama'a a Masallatai

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng