Bama-bamai sun tashi a jihar Borno

Bama-bamai sun tashi a jihar Borno

Rahotanni da Legit.ng ta samu daga wasu sanannun jaridun kasar nan sun bayyana cewa an samu fashewar bama - bamai a jihar Borno.

Jaridu, wadanda suka hada 'TheNation', gidan talabijin na TVC, SaharaReporters da sauransu, sun bayyana cewa bama - baman sun fashe ne a kauyen Konduga, lamarin da ya sa mazauna yankin gudun neman tsira da rayukansu.

SaharaReporters ta bayyana cewa bama - baman sun fashe ne da misalin karfe 8:38 na daren ranar Litinin.

A cewar SaharaReporters, wata majiya daga cikin jami'an tsaro ta sanar da ita cewa babu wani bayani a kan tashin bama - baman ko barnar da tashinsu ta haifar ya zuwa wanan lokaci.

Kazalika, majiyar ta ce mutane biyu sun mutu, kamar yadda SaharaReporters ta wallafa.

"An samu fashewar bama - bamai guda biyu a Mandirari Anguwan da misalin karfe 8:39 na daren an," a cewar majiyar SaharaReporters.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel