Muhimmin sako ga 'yan uwa Musulmai a kan daren Lailatul Qadri

Muhimmin sako ga 'yan uwa Musulmai a kan daren Lailatul Qadri

Daren Laylat al-Qadr, dare mai cike da alfarma, ya na wanzuwa ne a cikin kwanaki goma na karshen watan Ramadan, watan azumin addinin Musulunci.

Duk da cewa dukkan Musulmi sun yi amanna cewa ana riskar daren Lailatul Qadr ne a kwanaki 10 na karshen azumin Ramadan, babu wata rana takamaimai da aka bayyana cewa daren zai zo a cikinta.

Mafi yawan Musulmi sun raja'a a kan cewa daren Lailatun Qadr ya na zuwa ne a rana ta 27 ga watan Ramadan ko kuma daya daga cikin daren ranakun 21, 23, ko 25 na watan azumi.

Musulmi a dukkan fadin duniya kan rubanya aiyukan bautar Allah da suka hada da sallolin nafila da karatun Qur'ani mai girma a yammaci da daren ranakun goman karshen Ramadan.

A cikin daren Lailatul Qadri ne aka fara saukarwa da Annabi Muhammad Qur'ani a kogon Hira da ke wani tsauni a waje da birnin Mecca.

Mala'ika Jibrilu ya ziyarci annabi yayin da ya ke cikin kogon Hira tare da isar ma sa da sakon Ubangiji a kan ya fara karanta ayar farko da aka saukar ma sa daga cikin Qur'ani.

Tun bayan wannan daren Ubangiji ya cigaba da saukarwa annabi sakon ayoyin Qur'ani har tsawon shekaru 23.

A kowacce shekara, dubban Musulmai kan yawaita gabatar da Salla a cikin jam'i domin samun falalar da ke tattare da aiyukan lada a cikin kwanaki 10 na karshen azumi.

Wasu Musulman har tarewa su ke yi a manyan Masallatai (Ittikafi) domin samun sukunin mayar da hankali wajen bautar Ubangiji a kwanakin karshe na Ramadan.

Muhimmin sako ga 'yan uwa Musulmai a kan daren Lailatul Qadri

Musulmai a cikin Masallaci yayin azumi
Source: UGC

Saboda falalar da ke cikin daren Lailatul Qadri, sojojin kasar Israel su na barin Musulmai maza da mata da shekarunsu su ka wuce 50 su shiga Jerusalem domin gabatar da salloli da addu'o'i.

DUBA WANNAN: An raunata mutane 8 yayin rikici tsakanin 'yan Izala da Tijjaniyya a kan limancin Masallacin Juma'a

Wasu Musulman kan yi tattaki har zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da ibadu a Masallatan Makkah da Madina a cikin kwanakin karshe na azumi.

Sai dai, a cikin wannan shekarar, 2020, ma fi yawan Masallatai a fadin duniya an rufesu saboda bullar annobar korona.

Hakan ya tilasta Musulmi a kasashen duniya da dama hakura da gabatar da ibadu a Masallatai balle ma a samu damar zuwa Saudiyya.

A wannan karon, Musulmai su na gudanar da aiyukan ibadu daga gidajensu.

Amma, duk da hakan Musulmai a kasar Iran sun fita zuwa Masallatai a daren ranar Lahadi tare da gudanar da aiyukan ibada bisa biyayya ga tsarin nesanta da sauran matakan kare kai da dakile yaduwar annobar korona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel