COVID-19: Buhari ya yi taro da kungiyar gwamnonin kasar nan (Hotuna)

COVID-19: Buhari ya yi taro da kungiyar gwamnonin kasar nan (Hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi taro da kungiyar gwamnonin Najeriya wadanda suka samu jagorancin gwamna jihar Ekiti, Kayode Fayemi a yau Litinin, 18 ga watan Mayun 2020.

Kamar yadda shugaban kasar ya bayyana, sun tattauna ne a kan matsayar kwamitin yaki da cutar coronavirus na fadar sa.

Shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa ya umarci kwamitin yaki da cutar coronavirus ta fadar shi da su yi aiki tare da dukkan gwamnonin jihohi don samun shawo kan annobar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa akwai bukatar ilimantarwa tare da wayar wa jama'a da kai don su gane illoli da hanyoyin hana yaduwar muguwar cutar.

A cewar Buhari, "Na umarci kwamitin yaki da cutar coronavirus ta fada ta da su yi aiki tara da dukkan gwamnonin jihohin don samun shawo kan annobar."

Ya kara da cewa, "Akwai bukatar ilimantarwa da wayar wa da jama'a kai don su gane illolin cutar coronavirus tare da dakile hanyar yaduwarta."

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Buhari zai bayyana matakin dauka na gaba - Shugaban PTF

Hadimin shugaban kasa Buhari Sallau ya wallafa hotuna da bidiyon ganawar a shafin twitter inda ya ce:

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi taro da kungiyar gwamnonin Najeriya wadanda suka samu jagorancin gwamna jihar Ekiti, Kayode Fayemi a yau Litinin, 18 ga watan Mayun 2020."

Ga hotunan a kasa:

A gefe guda, mun ji cewa mai bada shawara ta musamman ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kafafen yada labarai, Femi Adesina, ya bayyana cewa shugaban kasar ba zai yi wani jawabi ga jama'a ba a yau Litinin, 18 ga watan Mayu.

Kamar yadda hadimin Shugaban kasar ya bayyana, kwamitin yaki da cutar coronavirus na fadar Shugaban kasa ne za su yi jawabi ga jama'a tare da bayyana matakin dauka na gaba.

Amma kuma idan za mu tuna, a jiya Lahadi ne Shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana cewa yau shugaban Buhari zai yi jawabi ga 'yan kasa.

A cewar Mustapha, shugaban kasar zai bayyana mataki na gaba da kasar za ta dauka na yaki da mummunar annobar.

Amma kuma a yau Litinin, hadimin shugaban kasa Buhari, Femi Adesina ya musanta hakan a wallafar da yayi a shafinsa na twitter.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel