Buhari ba zai yi wa 'yan Najeriya jawabi ba a yau - Fadar Shugaban kasa

Buhari ba zai yi wa 'yan Najeriya jawabi ba a yau - Fadar Shugaban kasa

Mai bada shawara ta musamman ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kafafen yada labarai, Femi Adesina, ya bayyana cewa shugaban kasar ba zai yi wani jawabi ga jama'a ba a yau Litinin, 18 ga watan Mayu.

Kamar yadda hadimin Shugaban kasar ya bayyana, kwamitin yaki da cutar coronavirus na fadar Shugaban kasa ne za su yi jawabi ga jama'a tare da bayyana matakin dauka na gaba.

Amma kuma idan za mu tuna, a jiya Lahadi ne Shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana cewa yau shugaban Buhari zai yi jawabi ga 'yan kasa.

Buhari ba zai yi wa 'yan Najeriya jawabi ba a yau - Fadar Shugaban kasa
Buhari ba zai yi wa 'yan Najeriya jawabi ba a yau - Fadar Shugaban kasa Hoto: The Cable
Asali: UGC

A cewar Mustapha, shugaban kasar zai bayyana mataki na gaba da kasar za ta dauka na yaki da mummunar annobar.

Amma kuma a yau Litinin, hadimin shugaban kasa Buhari, Femi Adesina ya musanta hakan a wallafar da yayi a shafinsa na twitter.

Ya wallafa a shafin nasa: "Babu jawabin Shugaban kasa a kan COVID-19 a yau. Ba a shirya kowanne ba. Maimakon haka, kwamitin Shugaban kasa kan yaki da annobar a yayin zantawarta na koda yaushe za ta sanar da kasar kan matakai na gaba."

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Hotunan 'yan ta'adda 20 da dakarun Najeriya suka halaka

A baya mun ji cewa a yau Litinin ne ake tsammanin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi a kan sabbin hanyoyin yakar annobar Coronavirus a kasar nan.

Jaridar The Nation ta bayyana cewa an yi wa shugaban kasar bayani a gidan gwamnati a kan inda kwamitin yaki da cutar coronavirus ta kasar nan suka tsaya.

Shugaban PTF, wanda shine sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da hakan bayan ziyarar da ya kai wa shugaban kasar a garin Abuja tare da kungiyarsa.

Shugaban kasar ya nuna gamsuwarsa a kan ci gaban da ake samu a yayin yakar cutar a kasar nan.

Shugaban PTF din ya samu rakiyar ministan lafiya Osagie Ehanire, shugaban NCDC Chikwe Ihekweazu da Dr Sani Aliyu.

Kamar yadda Mustapha ya bayyana, PTF ta soki gwamnatocin jihohin da suka bude wuraren bauta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel