Ministan kwadago ya bukaci ASUU ta janye yajin aiki kafin a sake zama a tebur
- Dole Malaman Jami’a su janye yajin aiki idan su na so su zauna da Gwamnati
- Ministan kwadago da samar da aikin yin Najeriya ya bayyana wannan mataki
- Chris Ngige ya ce bai kamata Malaman su yi yaji ana fama da COVID-19 ba
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sharadin sake zama a kan tebur da malaman jami’o’i da sunan cin ma yarjejeniya game da yajin aikin da ake yi a manyan makarantun kasar.
Mai girma Ministan kwadago da samar da aikin yi, Dr. Chris Ngige ya ce ya zama dole malaman makarantun su janye yajin aikin da su ke yi, idan su na so gwamnati ta zauna da su.
Ministan kasar ya bayyana wannan matsaya ne a ranar Asabar, 16 ga watan Mayu, 2020. Dr. Chris Ngige ya ce gwamnati ta yi na ta kokarin da ta biya ma’aikatan da ke yaji albashinsu.
Chris Ngige ya tabbatar da cewa kafin a kai ga yin wani zama tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU, sai malaman jami’ar sun kawo karshen yajin da su ka dade da tafiya.
KU KARANTA: Dalilin da ya sa na ce a biya Ma'aikata albashi da wuri - Gwamnan Bauchi
A cewar ministan, bai dace malaman jami’a su tattara su tafi yajin aiki a tsakiyar annobar COVID-19 ba, Ngige ya ce kamata ya yi ace malaman su na kokarin gano maganin cutar.
“Bai dace ba kuma abin haushi ne ace wadanda ya kamata su rika bincike game da magani da kayan aikin da za ayi amfani da su wajen warkar da cutar COVID-19 sun tafi yajin aiki”
Ministan na shugaba Buhari ya ke cewa a matsayin ‘yan kungiyar ASUU na ‘yan Najeriya, su na gida su na buga wasannin Ludo da Dara yayin da ake fama da annobar cutar COVID-19.
Kawo yanzu dai kungiyar ba ta maida martani ba, hakan na nufin malaman jami’an su na cigaba da yajin aiki duk da gwamnati ta soma biyan mafi yawansu bashin albashin da su ke bi.
Idan ba ku manta ba kwanan nan wani malami a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, farfesa Haruna Abdu Kaita, ya bayyana cewa su na kokarin gano maganin da zai warkar da Coronavirus.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng