Shugaban MURIC ya fitar da matsaya a game da shirin bude dakunan ibada

Shugaban MURIC ya fitar da matsaya a game da shirin bude dakunan ibada

Kungiyar nan ta MURIC da ke kare Musulmai a Najeriya, ta ja kunnen hukuma a kan batun bude masallatai domin cigaba da ibada a lokacin da ake tsakiyar fama da annobar Coronavirus.

Shugaban kungiyar ta MURIC, farfesa Ishaq Akintola ne ya yi wannan kira a wani dogon jawabi da ya fitar a ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, 2020, ya na ba gwamnatocin kasar shawara.

Kusan wannan shawara ta ci karo da rokon da malamai su ke yi a jihohin Arewa. MURIC ta soki matakan da wasu gwamnonin su ka dauka na bada damar cigaba da ibadu a cikin jama’a.

“Akwai rahotannin da mu ke ji cewa wasu jihohi sun bada damar bude masallatai, wannan ba dabarar kirki ba ce, dole mu bi a hankali da wannan cuta da ba a kai ga gano maganin ta ba.”

“Ka da musulmai su yi gaggawan kai kansu kabarinsu. Mu na bada shawarar cigaba da rufe masallatai har sai gwamnatin tarayya ta ce Najeriya ta tsira daga annobar.” Inji Akintola.

KU KARANTA: An yi karen-bata wajen rigimar addini a wani masallaci a Kogi

Shugaban MURIC ya fitar da matsaya a game da shirin bude dakunan ibada
Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola. Hoto: Facebook
Asali: UGC

Farfesan ya ce: “Mun san cewa dokar kullen ta na damun jama’a. Amma kuma haka ake fama da wannan a ko ina. Mu na rokon musulmai su kara hakuri. Wanda ya mutu, ya mutu kenan.”

Kungiyar ta kara da cewa idan ana so kowa ya tsira, sai an garkame ko ina: “Dole mu hada kai mu yaki cutar Coronavirus. Babu wata al’ummar da za ta iya fada da wannan cuta ita kadai”

“Za a iya fassara bude masallatai a wannan marra a matsayin janye hannu daga yaki da annobar. Hakan kuma na iya nufin yin fito na fito da dokar da gwamnati ta sa na haramta cinkoso.”

Shugaban MURIC ya ja-kunnen gwamnonin jihohin Borno, Gombe da Zamfara da su guji daukar matakin gaggawan da zai jawo matsala domin COVID-19 na iya yaduwa wajen sahun ibada.

MURIC ta ce ya kamata jihohin na Borno, Gombe da Zamfara su sake tunani kafin lokacin idi ya zo. A karshe kungiyar ta nemi a tuntubi sarkin Musulmi kafin a kai ga bude masallatai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel