Bayanai sun bayyana game da abin da ya sabbaba sallamar Sule Hunkuyi daga PDP

Bayanai sun bayyana game da abin da ya sabbaba sallamar Sule Hunkuyi daga PDP

Sabbin bayanai sun fara bayyana game da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta jahar Kaduna ta dakatar da Sanata Othman Suleiman Hunkuyi tare da mutanensa guda shida.

Daily Trust ta ruwaito sakataren watsa labaru na jam’iyyar, Ibrahim Alberoh Catoh ne ya fitar da sanarwar a ranar Asabar, 16 ga watan Mayu bayan wani zama da PDP ta yi a Kaduna.

KU KARANTA: Harin ta’addanci: Bom ta tashi da wani gwamna da masu gadinsa a cikin mota

A cewar sanarwar, PDP ta yi biyayya ga sashi na 57(3) na kundin tsarin mulkinta na shekarar 2017 wajen zartar da wannan hukunci a kan Suleiman Hunkuyi, tsohon Sanata Hunkuyi.

Sauran sun: Hashir Garba, Mato Dogara, Ibrahim Lazuru, John Danfulani, Lawal Imam Adamu da kuma Ubale Salmanduna. Sai dai PDP ba ta bayyana takamaimen laifin da suka aikata ba.

Bayanai sun bayyana game da abin da ya sabbaba sallamar Sule Hunkuyi daga PDP
Sule Hunkuyi Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Amma wasu majiyoyi daga PDP sun ce matakin baya rasa nasaba da shigar da jam’iyyar kara da Hunkuyi yayi jim kadan bayan an kammala zaben shuwagabanni a matakin mazabus.

Sakamakon haka kotu ta bayar da umarni ga jam’iyyar a kan cewa kada ta kuskura ta fitar da sakamakon zaben, wanda ya gudana a ranar 14 ga watan Maris.

Koda yake majiyar Legit.ng bata samu daman jin ta bakin Hunkuyi ba, amma John Danfulani ya bayyana cewa kwamitin bata da hurumin dakatar dasu ba tare da jin ta bakin su ba.

“Kwamitin gudanarwar ta ce ta dakatar damu ne saboda mun yi ma jam’iyya zagon kasa, wannan zance ka iya daukan kowanne irin ma’ana, don haka sai sun fayyace mana zamu gane.

“Amma akwai magana daya, basu da ikon dakatar da mu ba tare da sun ji ta bakin mu ba, don haka sun yi aikin banza saboda zan tunkari kotu a kan wannan maganar.” Inji shi.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Oyo a Najeriya, Seyi Makinde ya bayyana cewa sun garkame wani kamfani a jahar da aka samu ma’aikatanta su 30 dauke da cutar Coronavirus.

Gwamna Makinde ya bayyana haka ne a daren Lahadi, inda yace baya ga garkame kamfanin, zasu tsaftace ta ta hanyar yi mata feshin magani don kauce ma yaduwar cutar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel