Rikicin kabilanci: Fintiri ya saka dokar ta-baci a karamar hukumar Lamurde

Rikicin kabilanci: Fintiri ya saka dokar ta-baci a karamar hukumar Lamurde

- Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya saka dokar ta-baci ta sa'o'i 24 a karamar hukumar Lamurde bayan rikicin kabilanci da ya barke a wasu sassan yankin

- An tattaro cewa hankalin Gwamnan ya tashi da rikicin kuma ya tabbatar da cewa ba zai lamunci hakan ba

- Ya yi kira ga mazauna yankin da su yi watsi da tsegumi tare da samar da bayanai ga jami'an tsaro don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin

Gwamnatin jihar Adamawa ta saka dokar ta-baci ta sa'o'i 24 a karamar hukumar Lamurde bayan rikicin kabilanci da ya barke a wasu sassan yankin.

Sakataren yada labarai na Gwamna Ahmadu Fintiri, Humwashi Wonosikou, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi a garin Yola.

"Sakamakon samun tashin hankali a garin Tingno Dutse Tito, Sabon Layi da Bagashi, Gwamna Ahmadu Fintiri ya saka dokar ta-baci ta sa'o'i 24 a take.

"Gwamnati ta umarci mazauna yankunan da su kiyaye dokokin har sai sun sake jin wani bayani don tabbatar da zaman lafiya ya dawo yankin," Wonosikou yace.

Rikicin kabilanci: Fintiri ya saka dokar ta-baci a karamar hukumar Lamurde

Rikicin kabilanci: Fintiri ya saka dokar ta-baci a karamar hukumar Lamurde Hoto: NTA
Source: UGC

Ya ce hankalin Gwamnan ya tashi da rikicin kuma ya tabbatar da cewa ba zai lamunci hakan ba.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta bayyana, ya ja kunnen jami'an tsaro da su tabbatar da an kiyaye dokokin.

Ya yi kira ga mazauna yankin da su yi watsi da tsegumi tare da samar da bayanai ga jami'an tsaro don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta damka tallafin kayan abinci a tirela fiye da 120 ga gwamnatin Kano

"Yayin tabbatar da bada kariya ga dukiyoyi da rayukan jama'a, Fintiri ya shawarci mazauna yankin da su kwantar da hankulansu.

"Gwamnati na yin dukkan kokarin da ya dace don ganin an bankado masu assasa tashin hankalin," Wonosikou yace.

A wani labari na daban, gwamnatin Kaduna ta sanar da sauyi a ranaku biyu a cikin sati da ake sassauta dokar kulle jihar.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Muhammad Hafiz Bayero, manajan darektan kamfanin raya kasuwannin jihar Kaduna (KMDMC), gwamnatin ta ce za a sassauta dokar a ranakun 20 da 21 na watan Mayu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel