DHQ: ‘Yan Boko Haram da su ka tuba za su dawo cikin al’umma, ana samun masu mika wuya

DHQ: ‘Yan Boko Haram da su ka tuba za su dawo cikin al’umma, ana samun masu mika wuya

- Sojojin Boko Haram da su ka tuba za su koma cikin sauran Jama’an Gari

- John Enenche ya ce ana cigaba da samun ‘Yan ta’addan da ke mika wuya

Mun samu labari cewa rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa za ta saki wasu mayakan Boko Haram fiye da 600 da su ka tuba zuwa cikin al’umma a cikin watan Yuni mai zuwa.

Darektan yada labarai na gidan soji, Janar John Enenche ya ce tsofaffin mayaka 603 na Boko Haram da 'yan Operation Safe Corridor su ka canzawa tunani za su dawo cikin jama’a.

Janar John Enenche ya bayyana wannan a ranar Juma’a, 15 ga watan Mayu, 2020. Jami’in sojan ya ce wasu Mata 33 da kuma kananan yara 39 na ‘yan ta’addan sun shigo hannunsu.

Enenche ya ke cewa ‘yan ta’addan sun ajiye iyalan na su ne a ranar 19 ga watan Mayu a garin Ngala da ke jihar Borno. Sojojin sun bukaci ‘yan ta’addan su fito su mika wuyansu.

KU KARANTA: An samu wasu makamai a hannun 'Yan ta'adda a Jihar Nasarawa

Sojan ya shaidawa manema labarai cewa akwai wasu ‘yan ta’adda 280 da yanzu su ma ake kokarin canza masu tunani bayan da su ka mika kansu da kansu a gaban Dakarun soji.

A halin yanzu ana ta samun karuwar ‘yan ta’addan Boko Haram da su ke sallama kansu a hannun jami’an tsaro. Daga ciki har da mayakan kungiyar da su ka fito daga Jamhuriyar Nijar.

A jihar Adamawa, Dakarun Operation Lafiya Dole sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram 61 da ‘yan kunar bakin wake 3, an kuma yi nasarar yi wa wasu mayakan rauni inji Darektan sojin.

Bayan haka sojojin Najeriya sun yi nasarar kama wasu makamai da su ka hada da binidigogin AK-47 da harsashi na ‘yan ta’addan a yankin Agasha da ke cikin Guma a jihar Benuwai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel