Hadi Sirika: Gwamnati ta damke jirgin saman da ke kasuwanci a Najeriya

Hadi Sirika: Gwamnati ta damke jirgin saman da ke kasuwanci a Najeriya

- Gwamnatin Najeriya ta ce ta tare jirgi na kamfanin Ingila da ke daukar fasinjoji

- A halin yanzu Shugaba Muhammadu Buhari ya hana duk wani jirgin sama tashi

- Ministan kasar, Hadi Sirika ya ce za a hukunta wannan kamfani da ya saba doka

A ranar Lahadi, 17 ga watan Mayu, 2020, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwar cewa ta tare jirgin sama na wani kamfani a kasar Birtaniya da ke aiki a sararin samaniyar kasar.

An kama jirgin ne ya na cigaba da daukar fasinjoji a daidai lokacin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta haramta tashi da saukar duk wasu jiragen sama a fadin Najeriya.

Minista Hadi Sirika ya ce jirgin kamfanin Flair Aviation na kasar Birtaniya ne aka samu da laifin saba doka. Ba a ba wannan kamfani damar daukar fasinja ba inji ministan jiragen saman.

Mai girma ministan watau Hadi Sirika ya ce: “An ba wannan kamfani damar tashi domin zirga-zirgar taimakon jama’a ne, amma abin takaici sai mu ka kamu su, su na daukar fasinjoji.”

KU KARANTA: An wayi gari ba a sami wanda COVID-19 ta harba a Kano ba

Da alamu cikin fushi, sanata Hadi Sirika ya fitar da jawabi: “Wannan rashin sanin ciwon kan sauran jama’a ne! An tsare jirgin saman, ana kuma yi wa ma’aikatan ciki tambayoyi.”

Bayan haka, Sirika ya rubuta cewa za a hukunta kamfanin a dalilin jawo fushin hukumomin kasar da ya yi a wannan marra. “Akwai hukunci mai matukar tsauri da ya ke jiransu”

Ministan harkokin jiragen saman na Najeriya ya bayyana wannan ne duk a shafinsa na Tuwita. Wannan sanarwa ta zo da kimanin karfe 2:30 na ranar yau Lahadi a agogon Najeriya.

A karshen watan Maris gwamnatin tarayya ta rufe duk wasu filayen tashi da saukar jiragen sama. An dauki wannan mataki ne domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng