Gwamnonin Jihohi za su ba Ibrahim Gambari hadin-gwiwar aiki – Inji Fayemi

Gwamnonin Jihohi za su ba Ibrahim Gambari hadin-gwiwar aiki – Inji Fayemi

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun tabbatar da cewa za su bada cikakken goyon bayansu ga sabon shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Agboola Gambari.

Jaridar The Nation ta ce Kayode Fayemi ya rubutawa Ibrahim Agboola Gambari wasikar murna bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi shugaban ma’aikatar fadarsa.

Dr. Kayode Fayemi ya nuna farin cikinsa a madadin sauran gwamnonin kasar. A takardar, shugaban gwamnonin ya ce za su ba hadimin shugaban kasar duk wata hadin-gwiwa.

“A madadin sauran zababbun gwamnoni 36 na Najeriya a karkashin kungiyar NGF, na rubuta maka takarda in taya ka murkar nada ka da shugaban kasa Muhammadu Buhari GCFR ya yi a matsayin shugaban ma’aikatar fadarsa.”

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin sabon COS da Buhari ya nada, Ibrahim Gambari

Gwamnonin Jihohi za su ba Ibrahim Gambari hadin-gwiwar aiki – Inji Fayemi

Buhari da Fayemi ana gaisawa a Aso Villa. Hoto: Per Second News
Source: Twitter

“Kamar yadda ka sani, wannan nadin mukami ya na dauke da manyan nauye-nauye da hakkokai da su ke bukatar sanin aiki, tarbiyya, rikon amana, ke-ke-da-ke-ke da kuma lura da tsananin sadaukar da kai.” Inji gwamnan na Ekiti.

“Takardunka, da kwarewar ka da ayyukan da ka yi a baya a gida Najeriya da kasashen waje sun isa su bayyana kokarinka. A matsayinmu na gwamnoni, mun yi murna da wannan nadi.”

“Mu na nan a ko yaushe a jihohi domin mu yi aiki da kai yayin da ka ke kokarin gyara kasarmu a lokacin da aka shiga cikin wani hali na karyewar farashin mai a sakamakon annobar COVID-19.”

A karshen wasikar, Dr. Fayemi, ya ce: “Mu na yi maka addu’ar samun nasara a wannan muhimmin aiki mai nauyi da aka dauka.” Gambari ya shiga ofis ne a makon da ya gabata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel