Shugaban kasa ya sabunta wa’adin Akabueze a matsayin Shugaban ofishin kasafi

Shugaban kasa ya sabunta wa’adin Akabueze a matsayin Shugaban ofishin kasafi

- Benjamin Akabueze zai sake wasu shekaru hudu a ofis a Gwamnatin Tarayyya

- Ma’aikatar tattalin kudi ta tabbatar da an sabunta wa’adin na Darekta Janar din

- Akabueze ya fara rike wannan ofishi na kasafin kudi ne a watan Yuni na 2016

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sabunta wa’adin Mista Benjamin Akabueze a matsayin Darekta janar na ofishin kasafin kudin gwamnatin tarayyar Najeriya.

An fara nada Benjamin Akabueze a gwamnatin shugaba Buhari ne a matsayin Hadimi mai bada shawara a kan harkar kasafi da tsare-tsare a ranar 16 fa watan Fubrairu, 2016.

A watan Yuni, 2016 ne shugaba Muhammadu Buhari ya nada Benjamin Akabueze a kujerar Darekta janar na ofishin da ke kula da harkar kasafin kudi da tsare-tsaren tattali.

KU KARANTA: Buhari ya yi wa Iyalin tsohon Direbansa ta'aziyya bayan ya rasu

Shugaban kasa ya sabunta wa’adin Akabueze a matsayin Shugaban ofishin kasafi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari Hoto daga: Vanguard
Source: Twitter

Ma’aikatar tattalin arziki da kasafin kudin Najeriya ta tabbatar da sake nadin Benjamin Akabueze. Jaridar The Nation ba ta bada wani cikakken rahoto game da nadin da aka yi ba.

Ma’aikatar ta ce an sabunta wa’adin Ben Akabueze a ofis ne domin ya cigaba da irin kokarin da ya ke yi na inganta kasafin kudi da tabbatar da cewa gwamnati ta na bin tsare-tsaren.

Ben Akabueze masanin tattalin arziki ne wanda ya yi aiki a matsayin shugaban bankin Sterling Bank. Ya kuma rike kwamishinan kasafi na shekara takwas a gwamnatin Legas.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Ben Akabueze ya karanci ilmin Akawu ne a jami’ar Legas. Bayan nan ya yi karatun Digirgir a bangaren tattali da kuma kasuwanci duk a jihar ta Legas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel