COVID-19: Sarkin Daura ya yi nasiha mai ratsa zuciya bayan samun waraka

COVID-19: Sarkin Daura ya yi nasiha mai ratsa zuciya bayan samun waraka

A ranar Asabar ne sarkin Daura, Umar Faruq Umar ya tabbatar da cewa cutar coronavirus ba karya bace.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su ji tsoron Allah tare da bai wa gwamnatin tarayya da ta jihohi hadin kai don yakar annobar.

Basaraken ya yi wannan kiran ne a garin Katsina yayin da yake tsokaci a kan kwanciyar da yayi a asibitin gwamnatin tarayya da ke Katsina da kuma sallamarsa da aka yi daga baya.

Basaraken, wanda ya yi maganar da harshen Hausa yace, "Dukkan godiya da yabo na ga Allah da ya bamu ikon kawo wa wannan lokacin. Lokaci ne mai matukar hatsari a tarihin duniya baki daya.

COVID-19: Sarkin Daura ya yi nasiha mai ratsa zuciya bayan samun waraka

COVID-19: Sarkin Daura ya yi nasiha mai ratsa zuciya bayan samun waraka Hoto: TVC News
Source: UGC

"Ina so in janyo hankalin jama'a a kan wannan annobar da ta gallabi duniya. Ba wasa bace, mu ji tsoron Allah kuma mu koma gareshi.

"Idan duniya ba ta samu magani ba, kada mu yi tsammanin wani abu zai zo na gari. Lafiya uwar jiki ce.

"Ina son sanar da Gwamna cewa na warke sarai."

Ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Masari tare da ma'aikatan lafiya na jihar a kan taimakon da suka bashi a yayin da yake matukar bukata.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa an sallama basaraken daga asibitin gwamnatin tarayya na jihar Katsina a ranar Alhamis bayan kwanciyar da yayi na makonni biyu.

A gefe guda, gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tana fargabar akwai yiwuwar samun karuwar mace mace a kasar da ba su da alaka da coronavirus (COVID-19) tun bullar annobar a kasar.

Ta ce mafi yawancin mace macen suna faruwa ne saboda tsoro da wasu yan Najeriya ke yi na zuwa asibitoci inda za su samu kulawar da ta dace amma su ke kin zuwa don kada a gano suna da korona.

Ana kuma ganin cewa wasu daga cikin maaikatan lafiya suna kyashin duba marasa lafiya saboda tsoron kamuwa da cutar ta korona kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel