Shugaban Guinea Bissau ya kawo ma Buhari maganin Covid-19 na kasar Madagascar (Hotuna)

Shugaban Guinea Bissau ya kawo ma Buhari maganin Covid-19 na kasar Madagascar (Hotuna)

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karba bakuncin shugaban kasar Guinea Bissau

- Ya karbesa ne a fadar Aso Villa da ke babban birnin tarayyar Abuja, Najeriya

- Kamar yadda hotunan suka nuna, shugabannin sun kiyaye dokar nesa-nesa da juna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karba bakunci Shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissico Embalo a yau Asabar.

Ya karbesa ne a gidan gwamnatin tarayya da ke Aso Villa a babban birnin tarayyar Abuja.

Kamar yadda hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Twitter, an ga shugabannin kasashen biyu suna biyayya ga dokar nesa-nesa da juna.

Shugaba Buhari ya karba samfur din maganin cutar korona na gargajiya na kasar Madagascar daga hannun shugaban kasar Guinea Bissau.

Kasar Afrikan ta yi ikirarin cewa maganin na da karfin kashe kwayar cutar Korona.

Shugaba Buhari ya karba bakuncin Shugaban kasar Guinea Bissau
Shugaba Buhari ya karba bakuncin Shugaban kasar Guinea Bissau. Hoto daga Bashir Ahmad
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zamfara: An zartar da hukuncin kisa a kan mutumin da ya kashe mahaifiyarsa da yan uwansa mata biyu

Shugaba Buhari ya karba bakuncin Shugaban kasar Guinea Bissau
Shugaba Buhari ya karba bakuncin Shugaban kasar Guinea Bissau. Hoto daga Bashir Ahmad
Asali: Twitter

A yayin bayani a kan maganin, mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu, ya ce Buhari ya tabbatar da cewa zai yi biyayya ga kimiyya kafin fara amfani da maganin.

Babu dan Najeriya da zai yi amfani da maganin har sai an tabbatar da ingancinsa a kimiyyance..

"Kamar yadda shugaba Buhari ya tabbatar wa da Shugaba Umaro Sissioco na kasar Guinea Bissau, ya ce ba za a fara amfani da maganin gargajiyar har sai an tabbatar da ingancinsa," Garba Shehu yace.

"Muna da dokoki da tsarika a kasar nan. Duk wani ikirari ko magani da aka aiko da shi kasar nan, hukumomi za su tabbatar da ingancinsa. Ba zamu fara amfani da maganin ba har sai sun tabbatar da ingancinsa," Shugaba Buhari yace.

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Katsina ta dage dokar kulle da ta saka a baya a kananan hukumomin Mani da Safana a jihar kamar yadda This Day ta ruwaito.

Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya amince da dage dokar zaman gidan nan take kamar yadda yake cikin sanarwar da sakataren gwamnatin jihar, Dr Mustaha Inuwa ya fitar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164