Fadar shugaban kasa ta bada dalilin da yasa Buhari ba ya saka takunkumin fuska

Fadar shugaban kasa ta bada dalilin da yasa Buhari ba ya saka takunkumin fuska

- Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi bayanin dalilin da yasa shugaban kasar ba ya saka takunkumin fuska

- Fadar ta bayyana cewa shugaban kasar bai kamata ya saka takunkumin fuska ba tunda ya san inda yake babu cutar

- Amma kuma ana tsammanin kowanne bako da zai gana da shugaban kasar ya saka takunkumin fuskar

Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta musanta ikirarin da ake yi na cewa shugaban na karya dokar kiyaye yaduwar cutar korona ta hanyar kin saka takunkumin fuska.

Hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochia ce ta musanta zargin a ranar 16 ga watan Mayu a wata wallafa da tayi a shafinta na Twitter.

Kamar yadda Onochie ta bayyana, babu bukatar shugaban kasar ya saka takunkumin fuska saboda yana da tabbacin muhallinsa lafiya kalau yake.

Kamar yadda tace, ana tsammanin kowanne bako da zai kai ziyara fadar shugaban kasar ya saka takunkumin fuskar don bada kariya ga duk wanda zai yi mu'amala da shi.

Legit.ng ta bayyana cewa, ana ci gaba da cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani sakamakon hotunan Buhari da ake gani babu takunkumin fuska kuma yana al'amuran mulkinsa tare da wasu jami'ai.

Fadar shugaban kasar ta yi bayani gamsasshe game da hakan.

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai karya doka ba! Dokar masana harkar lafiya shine cewa idan kana a muhallinka da ke lafiya kalau, baka bukatar sanya takunkumin fuska.

“Wadanda ke ziyartan ka ne ya zama dole su sanya takunkumin fuska domin tabbatar da cewar basu bar kwayar cuta ba a muhallinka.

”Ana sanya takunkumin fuska ne domin kare mutanen da ke kewaye da mu,” in ji Onochie.

A gefe guda mun ji cewa, a ranar Alhamis, 15 ga watan Mayu, gwamnatin tarayya ta ce a yanzu sanya takunkumin rufe fuska ya zama tilas ga dukkanin al'umma a fadin kasar nan.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya sanar da hakan a ranar da ta gabata cikin babban birnin kasar na tarayya.

KU KARANTA KUMA: Ma’aikatan jinya 15 sun mutu daga cutar korona

Mista Mustapha shi ne shugaban kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa domin lura da annobar korona a Najeriya.

Sanarwarsa ta zo a yayin zaman karin haske kashi na 31 kan halin da ake ciki dangane da cutar korona a kasar.

Ya ce a yanzu amfani da takunkumin rufe fuska ba ra'ayi bane sai dai ya zama tilas gami da samun madogara ta shari'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng