COVID-19: Masari ya dage dokar kulle a kananan hukumomi biyu
Gwamnatin jihar Katsina ta dage dokar kulle da ta saka a baya a kananan hukumomin Mani da Safana a jihar kamar yadda This Day ta ruwaito.
Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya amince da dage dokar zaman gidan nan take kamar yadda yake cikin sanarwar da sakataren gwamnatin jihar, Dr Mustaha Inuwa ya fitar.
An saka dokar kullen ne a kananan hukumomin a ranakun 23 da 25 na watan Afrilun 2020 bayan samun bullar kwayar cutar COVID-19 kamar yadda gwajin da NCDC ta yi ya nuna.
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga suna can sun kai hari a Katsina
Sanarwar ta ce, "Gwamna Aminu Bello Masari ya yi wannan furucin ne a ranar Jumaa bayan samun rahoton cewa ba a sake samun sabon bullar cutar ba a kananan hukumomin biyu kuma wadanda suka kamu sun warke.
"Amma duk da haka, gwamnan ya yi kira ga alummar kananan hukumomin da sauran mutanen jihar su cigaba da ba da tazara tsakaninsu tare da amfani da takunkumin fuska da duk wasu dokoki da hukumomin tsaro da na lafiya ke bayarwa domin dakile yaduwar cutar."
A wani labarin, wata babbar kotu a jihar Zamfara ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani mutum da ya kashe mahaifiyarsa da yan uwansa mata biyu.
An gurfanar da Kamal Yusuf da wasu mutane biyu —Armayau Shehu da Caleb Humphrey a gaban kotu bisa zarginsu da aikata laifuka uku amma Humphrey ya mutu a gidan yari kafin a kammala sharia.
Laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa sun hada da hadin baki, fashi da makami da kisa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Da ya ke zartar da hukuncin, babban alkalin jihar, Mai sharia Kulu Aliyu ta yanke wa Kamal Yusuf hukuncin kisa ta hanyar rayata yayin da shi kuma mutum na biyu da ake tuhuma, Armayau Shehu an wanke shi an kuma sake shi.
Wanda aka yanke wa hukuncin yana da ikon daukaka kara a cikin kwanaki 90.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng