Zaratan sojin Najeriya sun ragargaza 'yan bindiga 27 a iyakar Katsina da Zamfara

Zaratan sojin Najeriya sun ragargaza 'yan bindiga 27 a iyakar Katsina da Zamfara

Rundunar sojin Operation Hadarin Daji tare da hadin guiwar dakarun sojin saman Najeriya sun halaka 'yan bindiga 27 tare da tarwatsa maboyarsu a tsakanin Nahuta da Doumborou da ke iyakar jihar Katsina da Zamfara.

A wata takarda da shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche ya sa hannu, ya ce sun kai farmakin ne a ranar 14 ga watan Mayu bayan bayanan sirri daga wata majiya da suka samu.

Bayanan sun bayyana cewa, shugaban 'yan ta'addan tare da mukarrabansa na wasu bukkoki kusa da yankin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce, dakarun sojin saman sun kai farmaki ta jirgin yakinsu, lamarin da ya kai ga kisan 'yan bindigar tare da Shanun da suka sace a yankin.

Kamar yadda Enenche ya bayyana, jiragen yakin sun ci gaba da ragargazar 'yan bindigar suna kashe su. Kadan daga ciki ne suka tsere da miyagun raunika.

Zaratan sojin Najeriya sun ragargaza 'yan bindiga 27 a iyakar Katsina da Zamfara
Zaratan sojin Najeriya sun ragargaza 'yan bindiga 27 a iyakar Katsina da Zamfara. Hoto daga HumAngle
Asali: UGC

KU KARANTA: Ta fallasu: Kun san jikakkiyar da ke tsakanin Ganduje da El-Rufai?

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai a ranar Juma'a ya yi taro da shugabannin cibiyoyin tsaro na jihar tare da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya kira taron ne don tattaunawa tare da shawo kan matsalar kashe-kashen da ke aukuwa a jihar ballantana na Kajuru da ya faru a makon da ya gabata.

A yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron a gidan gwamnatin jihar, Yakubu Umar Barde, dan majalisa mai wakiltar mazabar Chikun/Kajuru a tarayya ya yi kira ga jama'ar yankin da su zauna lafiya.

Barde, wanda dan jam'iyyar adawa ta PDP ne, ya ce gwamnan zai dauka dukkan matakan tsaron da za su kawo zaman lafiya a yankin.

Kamar yadda yace, "Mun tattauna halin tsaro da yankin Kajuru ke ciki ne tare da Malam Nasir El-Rufai tare da masu ruwa da tsaki.

"Akwai bukatar kabilu su yarda da juna. Idan babu zaman lafiya, ba za a samu yarda da juna ba. Gwamnan ya bukaci masu ruwa da tsaki da su yi wa jama'ar su magana don samun zaman lafiya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel