Romon damokaradiyya 10 da 'yan Najeriya za su mora bayan COVID-19 - Fadar shugaban kasa

Romon damokaradiyya 10 da 'yan Najeriya za su mora bayan COVID-19 - Fadar shugaban kasa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa tana shirya wasu tsare-tsare don tallafa wa 'yan Najeriya bayan annobar Coronavirus ta gushe.

Annobar ta shafi wasu sassan na tattalin arzikin kasar nan kuma ta durkusaf da kudin shiga gwamnati bayan faduwar farashin danyen man fetur warwas.

Najeriya ta dogara da siyar da danyen man fetur a matsayin inda kasar ta dogara da samu.

A matsayin hanyar tallafi, fadar shugaban kasa ta ce za ta mayar da hankali wajen samar da magunguna ta hanyar bincike a cikin gida tare da samar wa bangaren lafiya kayan bukata a cikin gida.

Romon damokaradiyya 10 da 'yan Najeriya za su mora bayan COVID-19 - Fadar shugaban kasa
Romon damokaradiyya 10 da 'yan Najeriya za su mora bayan COVID-19 - Fadar shugaban kasa Hoto: The Cable
Asali: UGC

Sauran tallafin an lissafo su ne a wata takarda da Femi Adesina, mai bada shawara na musamman ga Shugaba Buhari a fannin yada labarai yasa hannu.

Sun hada da:

1. Kungiyar tattalin arziki wacce ministar kudi, kasafi da tsari za ta shugabanta don duba illar da annobar ta yi wa tattalin arzikin kasar.

2. Kwamitin daidaituwar tattalin arziki wanda mataimakin shugaban kasa Yemis Osinbajo ke shugabanta don farfado da tattalin arziki bayan annobar.

3. Kwamitin da zai dinga lura da safarar amfanin gona wanda ministan aikin gona da raya karkarsa zai jagoranta.

4. Tsarin gyara ma'aikatar lafiyar kasar nan tare da samar da dakunan gwaji, dakunan kula na musamman da cibiyoyin killacewa.

5. Sabbbin tsare-tsare na masana'antar kudi da kuma tallafi ga bankuna kamar yadda babban bankin Najeriya ya bayyana.

6. Gagarumin shirin noma da kiwo.

7. Gagarumin gangamin samar da tituna a karkara.

8. Gagarumin gangamin samar da muhalli.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: An kama mutum 155 da suka saba dokar kulle a Sokoto

9. Za a fadada shirin tallafi da walwalar 'yan kasa.

10. Za a duba manyan ayyukan da za su ci kudi kadan kuma za su kammala da wuri.

A gefe guda, mun ji cewa mazauna karamar hukumar Faskari a jihar Katsina sun fara fitar da alkaluman irin ta'asar da 'yan bindiga ke tafkawa kowacce rana a jihar Katsina.

A ranar Laraba ne wasu 'yan bindiga dauke da mugayen makamai suka kai wani hari a kauyukan Daudawa da Angwan Baki a karamar hukumar Faskari, inda suka sace mutane biyar tare da kashe wasu mutane biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel