Boko Haram: NAF ta bayyana adadin sansanin da ta tarwatsa a cikin wata 3

Boko Haram: NAF ta bayyana adadin sansanin da ta tarwatsa a cikin wata 3

Rundunar sojin saman Najeriya ta yi nasarar tarwatsa matattarar 'yan Boko Haram 33 a cikin shekarar 2020.

Samamen da suka dinga kai wa ya dauka sa'o'i 1,700 inda suka halaka shugabannin kungiyar yan ta'addan.

Air Commodore Ibikunle Daramola, daraktan yada labarai da hulda da y na rundunar ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis. Ya bayyana cewa sun kai samame har sau 889 ta jiragen yaki.

A yayin bayani ga shugaban rundunar sojin saman, Air Marshal Sadique Abubakar, a hedkwatar NAF da ke Maiduguri a ranar Laraba, Air Commodore Precious Amadi ya ce ayyukansu na daga cikin aikin rundunar Operation Rattle Snake na biyu da na uku da kuma Operation Decisive Edge.

Boko Haram: NAF ta bayyana adadin sansanin da ta tarwatsa a cikin wata 3
Boko Haram: NAF ta bayyana adadin sansanin da ta tarwatsa a cikin wata 3 Hoto: The Nation
Asali: UGC

Amadi ya kara da bayyana cewa sun shiga cikin ayyukan rundunar sojin hadin guiwar da ke yakar 'yan ta'addan.

Ya kara da cewa, rundunar na ci gaba da samar da tallafi ta tudu da na sama ga rundunar dakarun hadin guiwa ta "Kantana Jimlan".

A jawabinsa, shugaban rundunar sojin na sama, Abubakar ya jinjinawa ATF din da ayyukan da suke yi na halaka 'yan ta'addan ta sama tare da tarwatsa sansaninsu.

Ya yi kira ga manyan hafsoshin da kuma sojojin sa kan su tabbatar da sun ci galaba ta har abada a kan 'yan ta'addan.

A yayin ziyarar, Abubakar ya kaddamar da sabon rukunin wurin zaman manyan hafsin sojojin saman.

KU KARANTA KUMA: Gambari ba zai iya shawo kan matsalar 'Cabals' ba a Najeriya - Farfesa Adibe

"NAF za ta ci gaba da tabbatar da cewa dakarun basu rasa wurin zama ba a yayin da suke aikinsu. Ina kira gareku da kada ku gaza wurin karasa 'yan ta'addan har sai kun kai su kasa har abada.

"Aikinmu ne kare Najeriya daga duk wani aikin ta'addanci. Kokarinku da sadaukantakarku na da matukar amfani. Ina tabbatar muku da cewa za a samar muku da duk wata walwala da ta dace," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng