Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wasu matasa marasa Imani

Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wasu matasa marasa Imani

Wata babbar kotun jahar Ribas ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wasu matasa da suka kashe karamar yarinya mai suna Victory Chikamso don yin tsafi da ita a shekarar 2017.

ThisDay ta ruwaito Alkalin kotun, mai sharia Adolphus Enebeli ne ya yanke hukuncin a kan Ifeanyi Maxwell Dike da Ugochukwu Nwamairo wanda ya nemi a kawo masa sassan jiki.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya umarci Musulmai su yi addu’o’in ganin bayan Corona a ranar Alhamis

Haka zalika kotun ta kama dansanda Sajan Johnbosco Okoronze da laifin taimaka ma Dike a lokacin daya tsere daga kurkuku bayan an kama shi, inda ta yanke masa daurin shekara daya.

A ranar 18 ga watan Agustan 2017 ne Dike ya murde wuyar karamar yarinya Victory, wanda kuma diya take a wajensa, a lokacin yana aji 2 a jami’ar UNIPORT inda yake karantar Physics.

Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wasu matasa marasa Imani

Dike Maxwell Hoto: ThisDay
Source: UGC

Dike ya kashe Victory ne a dakinsa dake unguwar Eliozo cikin karamar hukumar Obio/Akpor na jahar Ribas, sa’annan ya yanke wasu muhimman sassan jikinta.

Daga cikin sassan da ya cire akwai nono, farji, yatsu, kunnuwa, zuciya, kwayar ido da sauransu, a lokacin da yake hanyar zuwa binne gawarta da tsakar dare ne yan banga suka kama shi.

Daga bisani suka mika shi zuwa hannun hukumar Yansanda. Kotu ta kama Dike da Nwamiro da laifin hadin kai wajen aikata laifin kisa da kuma kisan kan.

Dike ya tabbatar ma kotun cewa Nwamairo ne ya nemi ya kawo sassan jikin yarinya da zuciyar mutum domin a yi masa tsafin da zai samu kudi malala gashin tinkiya.

Amma lauyan Dike, Lezina Amegwa bai musanta wanda yake karewa ya aikata laifin ba, sai dai kawai yace baya cikin hayyacinsa a lokacin da ya aikata laifin.

Don haka Alkali Enebeli yace a rataye Dike ta wuyansa har sai ya mutu, abokinsa kuma a rataye shi ta kafarsa, ma’ana kansa a kasa har sai ya mutu.

Alkali Enebeli yace ya yi ma Dansanda Jonhbosco sassauci ne saboda ya kwashe shekaru 2 a kurkuku, kuma an sallame shi daga aiki tun daga lokacin aukuwar lamarin.

Lauya mai kara, Chidi Eke ya bayyana farin cikinsa da hukuncin, inda yace kotu ta yi ma iyalan yarinyar adalci, amma lauyan Nwamairo, John Ndah yace zasu daukaka kara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel