Jagoran kungiyar IMN, El-Zakzaky ya kaddamar da shirin rabon abinci a Najeriya

Jagoran kungiyar IMN, El-Zakzaky ya kaddamar da shirin rabon abinci a Najeriya

- Ibrahim Yakubu El-Zakzaky zai rabawa mutane fiye da 100, 000 abinci

- Za a yi wannan rabo ne a duka Jihohi da babban birnin tarayya, Abuja

- Malamin ya kaddamar da wannan aikin tallafi duk da ya na gidan yari

Fitaccen jagoran mabiya addinin Shi’a wanda ya ke tsare a Najeriya, Ibrahim Yakubu El-Zakzaky, ya kaddamar da wani shiri na rabon abinci domin ragewa al’umma radadin da su ke ciki.

Ibrahim Yakubu El-Zakzaky ya soma rabon kayan tallafin ne a jiya, 13 ga watan Mayu, 2020. Daily Trust ta ce shehin ya na harin rabawa Bayin Allah 111, 000 a fadin kasar abin da za su ci.

Rahotanni sun ce an soma rabon kayan abincin nan ne a garin Kaduna, watau mahaifa kuma mazaunar babban malamin addinin. Wani na-kusa da shi ya ce duk shekara ya kan yi haka.

Mukhtar Abdullahi Sherrif wanda ya na cikin kwamitin masu rabon abincin ya shaidawa jaridar cewa a duk lokacin da watan Ramadan ya karaso, El-Zakzaky ya kan yi irin wannan rabo.

KU KARANTA: Abin da ya sa ba zan fito da El-Zakzaky ba - Gwamnan Kaduna

Jagoran kungiyar IMN, El-Zakzaky ya kaddamar da shirin rabon abinci a Najeriya
Ibrahim Zakzaky Hoto daga: Hindustani Times
Asali: Twitter

A yayin da Ibrahim El-Zakzaky da mai dakinsa Zeenat El-Zakzaky su ke daure a kurkukun garin Kaduna, Mukhtar Abdullahi Sherrif ne ya kaddamar da shirin a madadin jagoran na IMN.

“Sheikh Zakzaky ya saba raba abinci ga marasa karfi a lokacin da ya ke da ‘yanci, kuma ya cigaba da wannan al’ada. Haka wannan shekara ba za a samu wani banbanci ba.” Inji Sheriff.

Ya ce: “Mu na raba wadannan kayan abinci ne domin mu rage radadin da mutanen Najeriya; Musulmai da Kiristocinsu su ke ciki. Za mu raba kaso 3, 000 a kowace jihar kasar nan.”

Ba za a bar mutanen birnin tarayya a baya wajen wannan rabo da za ayi ba. Ya ce yanzu har sahun mutum 600 na farko da aka zaba a jihar Kaduna sun samu na su kayan abincin.

A karshe Abdullahi Sherrif ya ce: “Domin bin shawarwarin da masana kiwon lafiya su ka bada na gujewa yaduwar cutar Coronavirus, a duk rana za mu rika raba buhunan abinci 600 ne.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel