Zulum ya janye dokar kulle jihar Borno, ya umarci a bude Masallatai

Zulum ya janye dokar kulle jihar Borno, ya umarci a bude Masallatai

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da dakatar da dokar hana zirga - zirga da kulle jihar Borno sakamakon bullar annobar korona.

Ya janye dokar ne biyo bayan samun gagarumar nasarar da jihar ta yi a bangaren yaki da nnobar korona.

Mataimakin gwamnan Borno, Umar Kadafur, wanda shine shugaban kwamitin kar ta kwana a kan yaki da annobar a jihar, shine yasanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a daren ranar Larabara a Maiduguri.

"A cigaba da kokarin yaki tare da korar wannan mummunar annoba, wannan kwamiti ya na mai son sanar da jama'a cewa ya dakatar da dokar kulle gaba dayanta har sai abinda hali ya yi," a cewarsa.

Mista Kadafur ya ce an dakatar da dokar ne domin yin nazarin al'amura tare da bayyana cewa gwamnati ba zata yi sanya wajen mayar da dokar ba idan annobar ta sake yunkurowa.

Ya bayyana cewa amfani da takunkumin fuska a cikin jama'a ya zama wajibi.

Ya umarci jami'an gwamnati, masu rike da sarautar gargajiya, malaman addini da shugabanni a matakai daban - daban su tabbatar da cewa jama'a sun yi biyayya ga tsarin nesanta a wuraren ibada.

Ya tunasar da jama'a cewa har yanzu ba a yarda jama'a fiye da 20 su taru yayin jana'iza, daurin aure, ko radin suna ba.

Zulum ya janye dokar kulle jihar Borno, ya umarci a bude Masallatai
Farfesa Zulum
Asali: UGC

Ya bayyana cewa har yanzu ma'aikatan gwamnati da ke kan mataki na 1 zuwa na 12 zasu cigaba da aiki daga gidajensu.

Shugaban kwamitin ya umarci masu manyan shagunan magunguna da sauran cibiyoyin harkar lafiya su tura duk wani marar lafiya mai nasaba da annobar korona zuwa asibitocin gwamnati.

Ya yi gargadin cewa masu kunnen kashi za su fuskanci fushin doka.

DUBA WANNAN: An bude Masallatan kasar Iran albarkacin kwanaki 10 na karshen watan Ramadan

"Daga yanzu, za a iya cigaba da gudanar da Sallar Juma'a da sauran Salloli biyar a dukkan Masallatan jihar Borno da kwamitin Malaman jihar suka amince da su.

"Kazalika, za a gudanar da ibada a dukkan Coci - Coci da kungiyar Kiristoci (CAN) reshen jihar Borno ta amince da su," a cewar jawabin mataimakin gwamnan.

Mista Kadafur ya bayyana cewa za a dauki matakai na musamman a kan ababen hawa da za su shiga ko fita daga jihar Borno.

"Gwamnatin jihar Borno ta yi aiki da shawarar kwamitin Malaman jihar Borno, wadanda suka bayyana cewa Sallar Eidi Sunnah ce, ba dole ba, a saboda haka, babu sallar Eidi bayan kammala azumi. Ana bukatar Musulmai su kasance a gidajensu a wannan lokaci," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng