Annobar COVID-19: An killace Matafiya 50 da su ka bi ta Jihar Kaduna

Annobar COVID-19: An killace Matafiya 50 da su ka bi ta Jihar Kaduna

A ranar Talata, 12 ga watan Mayu, 2020, gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta killace wasu mutane da-dama a sansanin da ake ajiye masu hidimar kasa na NYSC da ke hanyar zuwa Abuja.

Mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna wajen yada labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye ya ce a ranar Lahadi aka fara kama wasu mutane 27 wadanda aka killace su a sansanin NYSC.

A ranar Litinin aka sake kawo wasu bakin mutane 23 cikin sansanin NYSC kamar yadda Mista Muyiwa Adekeye ya bayyana. Jaridar Daily Trust ta fitar da jawabin na hadimin gwamnan.

“Bayan ma’aikatan da aka halattawa zirga-zirga, daga yanzu duk wanda aka kama ya na shigowa garin Kaduna, za a maida shi ya koma inda ya fito.” Inji mai magana da yawun El-Rufai.

Gwamnatin jihar Kaduna ta kuma ja-kunnen gama-garin ma’aikatan gwamnatin tarayya da su ke yawon tafiya da iyalinsu daga Kaduna zuwa garin Abuja da cewa su daina bin hanyar.

KU KARANTA: COVID-19: Wani babban mutumi ya mutu a Jihar Kaduna - El-Rufai

Annobar COVID-19: An killace Matafiya 50 da su ka bi ta Jihar Kaduna
Gwamnan Kaduna. Hoto: Jaridar Sun
Asali: Twitter

Gwamnatin Nasir El-Rufai ta ce saba dokar da wadannan ma’aikata su ke yi bai dace ba. Idan ba ku manta ba gwamnati ta haramtawa kowa fita face malaman asibiti da jami’an tsaro.

A jawabin da gwamnan ya fitar, ya gargadi duk masu sabawa takunkumin da gwamnati ta sa saboda cutar COVID-19. El-Rufai ya ce zai kama duk wanda ya saba doka ya killace sa.

“A daina amfani da motocin gwamnati da takardu da khaki wajen saba doka ko kuma domin a samu kariya daga matakan da shugaban kasa Buhari ya kafa na takaita zirga-zirga."

A karshe gwamnatin jihar Kaduna ta fadawa talakawa cewa su daina kauracewa gwajin cutar COVID-19, gujewa gwajin zai iya jefa al’umma a cikin hadarin kamuwa da Coronavirus.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel