Mutum 20,000 ka iya kamuwa da korona a Jigawa – Gwamna Badaru

Mutum 20,000 ka iya kamuwa da korona a Jigawa – Gwamna Badaru

Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa ya bayyana cewa mutum 20,000 ka iya harbuwa da cutar coronavirus a jiharsa.

A wata hira da ya yi da sashin Hausa na BBC, gwamnan ya bayyana cewa idan mutanen jihar suka bijire wajen bin ka'idojin da aka saka na kare kai daga kamuwa da cutar, adadin zai kai 20,000, amma idan kuma aka bi ka'idoji, mutane ba za su wuce 800 ba.

Gwamnan ya bayyana cewa an sassauta matakai na kulle a jihar inda cikin kananan hukumomi takwas da aka rufe sakamakon cutar an bude biyu.

Gwamnan ya kara da cewa a halin yanzu sauran kananan hukumomi shida da ke a rufe za su iya gudanar da sallar Juma'a, amma akwai ka'idoji da aka saka wadanda masallatai za su bi.

Mutum 20,000 ka iya kamuwa da korona a Jigawa – Gwamna Badaru

Mutum 20,000 ka iya kamuwa da korona a Jigawa – Gwamna Badaru Hoto: Badaru Abubakar
Source: Twitter

Cikin matakan har da bayar da tazara a cikin masallaci da kuma wanke hannu kafin shiga.

A wani labarin na daban, mun ji cewa kungiyar farfesoshi daga sashen hada magunguna na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ta ce ta samo maganin cutar coronavirus.

A yayin zantawa da jaridar Daily Trust a ranar Laraba, daya daga cikin masu binciken, Farfesa Haruna Abdu Kaita, ya ce sun samo maganin cutar COVID-19 daga tsirrai da ake samu a wasu sassan kasar nan.

Wannan labarin na zuwa ne bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin shigo da maganin korona na gargajiya wanda kasar Madagascar ke amfani da shi don riga-kafi da kuma maganin cutar.

KU KARANTA KUMA: Tsohon kwamishinan Kano ya ba da labarin wahalar da ya sha yayin fama da cutar korona

Jama'a da dama sun kalubalanci hukuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari ciki har da kungiyar masu hada magunguna ta Najeriya.

Sun kwatanta hakan da cin zarafi ko tozarci ga masu hada magunguna, masana kimiyya da kuma masu bincike.

Kaita ya ce nan ba da dadewa ba za su fitar da maganin bayan sun tabbatar da nasararsa wajen kashe kwayar cutar a jikin dan Adam.

Ya ce bayan sun fitar da maganin, za su sanar da kowa tsirran da suka yi amfani dasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel