Gambari: Abinda 'yan Najeriya za su yi tsammani daga gareni

Gambari: Abinda 'yan Najeriya za su yi tsammani daga gareni

Sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya ce abinda zai bai wa fifiko na farko shine biyayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ba jama'a ba.

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ya sanar da hakan ne yayin da yayi tattaunawa takaitacciya da manema labaran gidan gwamnati a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Ya fara da mika sakon godiyarsa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ga cancantarsa na mate wannan gurbin. Ya ce zai yi iyakar bakin kokarinsa wajen hidimtawa shugaban kasar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Gambari: Abinda 'yan Najeriya za su yi tsammani daga gareni

Gambari: Abinda 'yan Najeriya za su yi tsammani daga gareni Hoto: Bashir Ahmad
Source: Twitter

"Ina mika sakon godiyata ga shugaban kasar Najeriya da ya bani wannan damar ta hidimta masa da kuma kasa ta baki daya," yace.

A yayin da manema labarai suka tambayesa game da abinda za a yi tsammanin zai yi a matsayin sa na shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar, ya ce "Ba mu fara aiki ba, sai na bincika. Ba ga 'yan kasa kai tsaye zan yi aiki ba, ga shugaban kasa zan yi".

A kan abinda yake da shi da zai amfanar da shugaban kasar, ya ce "Biyayyata, kwarewata da kuma taimakona."

Ya kara da cewa babban abinda zai kiyaye a matsayin sa na shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar shine hidimta wa shugaban kasar iyakar iyawarsa.

KU KARANTA KUMA: Shugaban ma’aikatan Villa: Gwamna Abdulrazak ya gode ma Buhari bisa nadin Gambari

A baya mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shugabanci taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a fadarsa da ke Abuja inda ya bayyana Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan sa.

Taron da aka yi ta yanar gizo shine na farko irinsa da aka taba yi. Mataimakin shugaban kasa, sakataren gwamnatin tarayya da wasu ministoci duk sun halarci taron ta yanar gizo.

Wadanda suka halarci taron sun hada da shugabar ma'aikata, Folashade Yemi-Esan wacce ta bayyana a taron ta yanar gizo.

Taron ya fara wurin karfe 11:22 na safe inda aka fara tattaunawa a kan annobar Coronavirus da ta addabi kasar nan, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel