Kaduna: Shugaban kasa ya koka da kashe-kashen da ake ta yi a Yankin Adara

Kaduna: Shugaban kasa ya koka da kashe-kashen da ake ta yi a Yankin Adara

A ranar Talata, 12 ga watan Mayu, 2020, ‘yan sandan Najeriya su ka tabbatar da cewa an kashe wasu mutane kimanin 15. Ana zargin makiyaya Fulani ne su ka kai wannan harin.

Kamar yadda jami’an tsaro su ka bayyana, an yi wannan ta’adi ne a wani kauyen da ake kira Gonan-Rogo a kauyen Kufana da ke cikin karamar hukumar Kajuru, a jihar Kaduna.

Shugaban kasar ya fitar da jawabi ne ta bakin mai taimaka masa wajen harkokin yada labarai da hulda da jama’a watau Malam Garba Shehu a jiya Talata da kusan karfe 10:30 na dare.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake yin Allah-wadai da wannan abu da ya faru, ya na mai sukar hare-haren fari da ramuwar gayya da ake yi tsakanin Fulani da mutanen Addara.

Shugaban kasar ya ke cewa: “Kashe mutane da sunan ramuwa ba daidai ba ne.” Ya ja kunnen mutane su daina daukar doka a hannunsu, ya ce babu wanda doka ta ba wannan dama.

KU KARANTA: Mutanen Garin Chikucn sun tsere bayan an shiga halin dar-dar

“Yunkurin tashi a kare kai da kai a maimakon bin abin da doka ta ce shi ne ainihin abin da ya ke jawo yawon kashe-kashen da ake samu tsakanin al’ummar nan biyu.” Inji Buhari.

A karshen jawabin na sa, Malam Shehu ya ce: “Shugaban kasa (Muhammadu Buhari) ya yi gargadin cewa babu wani Bawan Allah da ke da hurumin daukar doka a hannunsa.”

A sakamakon yawan kashe-kashen da ake yi a Kajuru, kwanaki Adarawa su ka yi kira ga shugaban kasa ya kafa kwamitin musamman da zai yi bincike kan silar rikici-rikicen.

A daidai wannan lokaci kuma mun samu labari cewa ana kukan ana ta fama da kashe-kashe a jihar Katsina a cikin ‘yan kwanakin nan, amma shugaban kasa bai ce komai ba tukun.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel