Yanzu Yanzu: Buhari ya bayyana Gambari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadarsa, ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Yanzu Yanzu: Buhari ya bayyana Gambari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadarsa, ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin shugaban ma’aikatansa

- Shugaban kasar da kansa ne ya tabbatar dashi a ranar Laraba, 13 ga watan Mayu

- Harma Gambari ya halarci zaman majalisa na farko a fadar shuaban kasa, Abuja

A karshe, fadar shugaban kasa ta tabbatar da Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Farfesa Gambari ya kama aiki a matsayin shugaban ma’aikatan Buhari bayan an gabatar da shi a gaban majalisar zartarwa lokacin ganawarta a ranar Laraba, 13 ga watan Mayu, Channels TV ta ruwaito.

Sakataren din-din-din na majalisar, Alhaji Tijani Umar, ya zaga da sabon shugaban ma’aikatan tarayyan don ganin gine-ginen fadar shugaban kasar.

Taron ya fara wurin karfe 11:22 na safe inda aka fara tattaunawa a kan annobar Coronavirus da ta addabi kasar nan, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: 'Yan bindiga sun sace babban hafsin soja

An yi taron ne ta hanyar kiyaye dokar nesa-nesa da juna wacce ta zama doka ta farko da aka fara bi a taron.

An yi shiru na minti daya don karrama marigayi Malam Abba Kyari da wasu 'yan majalisar kafin a fara taron yayin da sakataren gwamnatin tarayya ya bayyana Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar.

Gambari ya zauna a kujerar da aka tanada don shi wacce ke kusa da ta shugaban kasa Buhari bayan an gabatar da shi.

A baya mun ji cewa Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan nada Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadarsa.

Gambari, wanda farfesan kimiyyar siyasa ne kuma tsohon wakilin Najeriya a majalisar dinkin duniya dan asalin jihar Kwara ne.

A wata takarda da ta fita a ranar Laraba, Sulu-Gambari ya kwatanta nadin da babban karramawa ga jama'ar Ilorin da Kwara gaba daya.

Ya ce zaben Gambari a wannan matsayin zai bayyanar da kwarewarsa tare da gogewarsa a fannin mulkin wanda zai kasance babbar gudumawa ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel