COVID-19: Rashin yarda da cutar tare da taurin kai ke damun mutanen jiha ta - Gwamnan Bauchi

COVID-19: Rashin yarda da cutar tare da taurin kai ke damun mutanen jiha ta - Gwamnan Bauchi

Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya bayyana cewa mazauna jihar basu yarda da wanzuwar cutar ba duk da kuwa ya yi jinyar ya tashi.

A yayin zantawa da gidan Talabijin na NTA a ranar Litinin, 11 ga watan Mayu, Gwamna Bala Muhammad ya ce rashin yarda da cutar da taurin kai irin na jama'ar jihar na daga cikin abinda ke bada gudumawa a matsalolin jihar.

Ya ce: "Daga cikin matsalolin da muke da shi a jihar, akwai rashin yarda da wanzuwar cutar da kuma taurin kan mutane.

"Na sanar dasu, ta yuwu wata hanyar taimako ce Allah ya fara dora min cutar a jihar. COVID-19 ba ta damu da ko kai waye ba kuma na yi nasarar warkewa.

"A don haka, ina kira ga jama'a da su dauka cutar da gaske. Mun rufe masallatai da majami'u. Mun hana sallar Juma'a da sauransu. Mun hana zuwa kasuwanni idan na a saka takunkumin fuska ba."

COVID-19: Rashin yarda da cutar tare da taurin kai ke damun mutanen jiha ta - Gwamnan Bauchi

COVID-19: Rashin yarda da cutar tare da taurin kai ke damun mutanen jiha ta - Gwamnan Bauchi Hoto: Sanator Bala A. Mohammed
Source: Twitter

A kan amfani da Chloroquine don maganin korona, ya ce: "Ban ce Chloroquine na maganin korona ba. Ni ba likita bane kuma ba jahili bane ballantana in fitar da magani in ce a sha. Ba ni da wannan damar."

KU KARANTA KUMA: Jerin Jihohin da su ka samu fiye da Jakada guda a sababbin nade-naden da aka yi

A gefe guda gwamnan Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayar da umarnin cigaba da gabatar da sallar Juma'a a Masallatan jihar da aka rufe sakamakon bullar annobar korona.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da ya ke sanar da sallamar da masu jinyar korona 7 da aka sallama daga cibiyar killacewa ta jihar Jigawa bayan an tabbatar sun warke sarai.

Ya sanar da hakan ne yayin taro da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

A cewar gwamna Badaru, ya amince da bude Masallatan ne bayan ganawarsa da kungiyar malamai ta jihar Jigawa.

Ya ce sun cimma yarjejeniyar cewar za a bi dukkan matakan dakile yaduwar kwayar cutar korona a Masallatan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel