An sallami masu jinyar korona 39 bayan sun warke sarai a Gombe

An sallami masu jinyar korona 39 bayan sun warke sarai a Gombe

Kwamitin kar ta kwana a yaki da annobar korona a jihar Gombe ya sanar da cewa an sallami masu jinya 39 daga cibiyar killacewa bayan sakamakon gwajinsu ya nuna cewa yanzu basa dauke da kwayar cutar.

Ya zuwa yanzu an sallami jimillar mutane 39 daga cibiyar killace masu dauke da kwayar cutar korona a jihar Gombe.

Shugaban kwamitin, Idris Mohammed, ya bayyana cewa an sallami mutane biyar ranar Litinin, yayin da aka kara sallamar wasu 34 ranar Talata bayan sakamakon gwajinsu da aka aikawa NCDC ya nuna cewa basa dauke da kwayar cutar korona.

Ya ce, a karo na farko, an sallami masu jinyar korona 20 daga cibiyar a ranar Asabar din da ta gabata. Sannan, ya kara da cewa an sallami jimillar mutane 59 da yanzu haka sun koma cikin iyalansu.

Ya ce an samu jimillar mutane 118 da ke dauke da kwayar cutar a Gombe bayan gwamnatin jihar ta aika da jinin mutane 1,168 dakin gwajin NCDC da ke Abuja.

Kazalika, ya bayyana cewa mutum daya ne ya mutu a jihar Gombe sakamakon annobar cutar korona.

An sallami masu jinyar korona 39 bayan sun warke sarai a Gombe
An sallami masu jinyar korona 39 bayan sun warke sarai a Gombe Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Kwamishinan lafiya na jihar Gombe, Dakta Ahmed Gana, ya ce ana sallamar mutane da yawa daga cibiyar ne saboda wani sabon tsari da NCDC ta bullo da shi.

DUBA WANNAN: Cocin katolika ta mika dukkan asibitocinta 245 ga FG don a yaki annobar korona

A cewarsa, yanzu za a iya sallamar mai jinyar korona bayan sakamakon gwaji koda daya ne ya nuna cewa ba ya dauke da kwayar cutar.

"Bisa sabon tsarin hukumar NCDC, za a iya sallamar mai jinyar cutar korona daga cibiyar killacewa bayan sakamakon gwaji daya ya nuna cewa ba ya dauke da kwayar cutar, sabanin gwaji biyu da ake yi a baya," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel